logo

HAUSA

An rufe gasar wasannin sojoji ta duniya karo na 7, yan wasan Afrika suna iyakacin kokarinsu cikin gasa

2019-11-05 10:47:36 CRI

An rufe gasar wasannin sojoji ta duniya karo na 7 na wa'adin kwanaki 10, a daren jiya Lahadi a cibiyar wasannin motsa jiki ta birnin Wuhan, an kuma kwantar da wutar yula. Sojoji 'yan wasan motsa jiki sama da 9300 daga kasashe 109 sun yi kece rani da juna, an ce wannan gasa ta zama wani dandalin bayyana fasaha da kuma kara dankon zumunci tsakanin sojojin kasa da kasa. Bikin nuna wake-wake da raye-raye na rufe gasar ya kasu kashi biyu. Na farko an yi masa lakabin "Mun hadu tare", inda aka waiwayi yadda aka gudanar da gasanni a zagaye 6 da suka gabata, da ci gaban da aka samu, na biyu kuma mai taken "Wuhan na maraba da kai", alamar musamman na gasar "Bin Bin" ya gayyaci bakin ketare da su ganewa idonsu al'adun gargajiya na kasar Sin da bude ido a Wuhan, don fahimtar yadda Sin take kasancewa a sabon karni. A wannan gasa kuma, Sojoji 'yan wasan motsa jiki sama da 9300 daga kasashe 109 sun fafata da juna cikin gasanni 27, inda aka samar da lambobin yabo na zinari 329. Tawagar Sin, Rasha da Brazil suna sahun gaba a fannin samun lambobin yabo, tawagoginsu fiye da 60 ne suka samu lambobin yabo. Tawagar sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ta samu lambar yabo ta zinari 133, da ta azurfa 64 da ta tagulla 42, sakamakon da ya sa Sin ta kai matsayin farko a fannin lambar yabo ta zinari da kuma yawan lambobin yabo, har wannan adadi ya kafa wani matsayin bajinta a tarihin wannan gasa. Dadin dadawa, an kuma gabatar da gasannin 'yan wasan motsa jiki na nakasassu na wasan guje-guje da tsalle-tsalle da wasan harbe-harbe, inda aka samar da lambar yabo ta zinari 31, wasan harbe-harbe kuma ya samar da lambar yabo ta kungiya na 'yan wasan motsa jiki na nakasassu. Yayin wannan gasar, 'yan wasan sun karya matsayin bajintar duniya har sau 7, kuma karya matsayin bajintar gasa irin wannan sau 85. Babban sakataren majalisar gudanarwa ta gasar sojojin kasa da kasa Dorah Mamby Koita ya ce: "'Yan wasan sun yi iyakacin kokarinsu cikin gasar, har wasu sun kai matsayin koli, suna karya matsayin bajintar wasan sojojin kasa da kasa, musamman a fannin wasan iyo, wasan harbe-harbe da wasan guje-guje da tsalle-tsalle. Saboda wasannin gasar muhimman matakai ne daga cikin wasannin gasar sojoji, muna farin ciki da kuma alfahari, matakin da ya nuna cewa, sojojin kasa da kasa suna kokarin taka rawa cikin wannan gasa." Kasar Rasha ta kai matsayi na biyu ta fuskar lambobin yabo, bisa lambar yabo ta zinari 51, ta azurfa 53 da kuma ta tagulla 57. Daga cikinsu kuma, tawagar wasan yin saukar laima ta sojin Rasha ta sami lambar yabo 15. Mai jagorancin tawagar Aleksandr Ivanov ya taya kasar Sin murna kan ci gaba da kasar ta samu cikin gasar. Ya ce, 'yan wasa sojojin kasar Sin suna da karfi sosai, kuma gasar da aka yi a wannan karo ta fi kyau a tarihi, ya ce: "kyakkywan Shirin da aka yi wa gasar da kuma takara mai ban sha'awa tsakanin 'yan wasa, sansanin 'yan wasa inda ake samun muhalli mai kyau, da abinci mai dadi da dai sauransu sun ba ni mamaki sosai. Gasar a wannan karo ta fi kyau a tarihi. Muna jin dadi sosai, kuma muna godiya ga mazauna birnin Wuhan bisa taimakon da suka ba mu. Wannan gasar ta zama wata gaggarumar wasan motsa jiki wadda kuma ke kara zumunci." Jagoran tawagar kasar Bosnia and Herzegovina Emir Kliko na ganin cewa, shirin da Sin ta yi a wannan karo da kuma ci gaban kasar, sun ba shi mamaki matuka, ya ce: "Ba zan manta da gasar wannan karo ba, musamman ma Sinawa sun nuna mini kauna kuma sun yi maraba da mu kwarai da gaske. Tsarin gasar ya yi kyau sosai. A Sa'i daya kuma, bunkasuwa da kuma zamanintarwar kasar Sin na ba ni mamaki matuka." Sojoji 'yan wasannin kasashe daban-daban suna kokarin kece raini da juna cikin gasanni, kuma sun kulla dankon zumunci tsakaninsu. Gasar a wannan karo dai ta zama wani gaggarumin biki na yin takara yadda ya kamata, da yin taro cikin lumana, da musayar al'adun aikin soja, matakin da ya sa aka bayyana gasar soji a matsayin wani dandalin "Kara dankon zumunci ta hanyar wasan motsa jiki" a Wuhan. Shugaban majalisar gudanarwa ta gasar sojin kasa da kasa kanar Herve Piccirillo ya ce: " 'Kara dankon zumunci ta hanyar wasan motsa jiki' ba kawai wani kira da aka yi ba ne, ya zama muradun gasar sojin kasa da kasa. Mambobin sojojin kasashe fiye da dari suna kokari cimma wannan muradu. Yayin gasar, ana mutunta tunani, addini da ra'ayin kowa, kuma tunanin kokarin hadin kansu tare da sanin bambanci dake tsakaninsu, zai amfanawa rundunonin kasa da kasa nan gaba. Sojojin kasa da kasa suna kara zumuncinsu babu rigingimu kuma babu nuna karfin tuwo. Gobe za su karbi wutar yula daga hannunmu, kuma za su sauke nauyin dake wuyansu wajen ci gaba da yada wutar yula, don tunawa da wannan gaggarumin biki." Shugabar kwamitin shirya gasa a wannan karo, kuma mambar ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS kana mataimakiyar firaministan kasar Sin Madam Sun Chunlan ta yi jawabi a wajen bikin rufe gasar, inda ta ce, gasar a wannan karo wani gaggarumin biki ne na kara zumunci, da samar da zaman lafiya cikin hadin kai, dake bayyana halayen sojojin kasa da kasa da kuma samun ci gaba mai armashi. Kuma ta yi kira da a hada kai don samar da wata damar karawa juna sani ta hanyar wasan motsa jiki, ta yadda za a kara tuntubar jama'ar kasa da kasa don ba da babbar gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya da ingiza raya kyakkyawar makomar Bil Adama bai daya. An ce, karon farko ke nan da aka gudanar da irin wannan gasa ba a cikin sansanin soja ba, kuma karon farko da aka gina sansanin gasar, aka kuma gudanar da ita a birni 1 Shugaban kwamitin shirya gasar a wannan karo kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS, kana mataimakin kwamitin soja na JKS Xu Qiliang ne ya sanar da rufe biki a wannan karo, daga baya kuma aka yi kidan gasar. Shugaban majalisar gudanarwa ta gasar sojin kasa da kasa kanar Herve Piccirillo ya karbi wutar yula da kuma tutar gasar daga magajin garin Wuhan Zhou Xianwang, kuma an kwantar da wutar yula dake cibiyar filin wasan motsa jiki na Wuhan, hakan ya kawo karshen gasar a wannan karo na kwanaki 10. (Amina Xu) An yi gasar wasan Taekwondo na matsayin 87 kg tsakanin maza wato nauyin dukkan 'yan wasan da suka shiga gasar bai kai kilogiram 87 ba. Dan wasan kasar Nijeriya Ahmed Shehu Bello bai ci nasara cikin gasar da ya yi da Suaza Gil David Antonio na kasar Colombia ba, bai kasance cikin 'yan wasa 8 mafiya karfi cikin gasar ba. Bayan gasar, wakiliyarmu Tasallah Yuan ta tambaye shi ra'ayinsa kan gasar da ya yi a yau, shirinsa a nan gaba da ayyukan da kasar Sin ta yi wajen shirya gasar. Baya ga Ahmed Shehu Bello kuma, dan wasan kasar Nijer Oumarou Ibrahim shi ma bai taki sa'a cikin gasar da ya yi da takwaransa na kasar Iran Abbasi Mardekheh Babak ba. Shi ma bai kasance cikin 'yan wasa 8 mafiya karfi ba. Bayan gasar, wakiliyarmu Tasallah Yuan ta tambayeshi ra'ayinsa kan gasar da ya yi a yau, ayyukan shiryawa da shirinsa a nan gaba.

Ban da wanann kuma, kwamanda Nuhu Jidere Bala, babban jami'in kungiyar 'yan wasa sojoji ta kasar Nijeriya ya jinjina wa kasar Sin bisa ayyukan shirya gasar. (Tasalla Yuan)