Takardar bayani game da wadatar abinci a kasar Sin
2019-10-24 08:41:17 CRI
A kwanakin baya ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani kan wadatar abinci a kasar, inda ta yi bayani kan kokarin da kasar ke yi a fannin inganta wadatar abinci da ma fadada dangantakarta da kasashen waje a wannan fanni.
Duk da raunin da kasar take fuskanta a fannin aikin gona da kangin talauci, JKS dake jagorancin kasar ta kaddamar da wani gangamin fadakar da jama'a game da kara zage zamtse a shekaru 70 din da suka gabata, wanda ya sanya kasar zama mai wadatar abinci a duniya.
A hannun kuma, yayin da duniya ke fama da kalubalen wadatar abinci, inda mutane sama da miliyan 800 ke fama da matsalar yunwa, wasu sassan duniya na kawo matsala ga cinikayyar abinci ta hanyar ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra'ayi na kashin kai
A yayin da take kokarin samar da issashen abinci a cikin gida, kasar Sin za ta hada kai da sauran kasashen duniya wajen ganin an kawar da matsalar yunwa baki daya. A cewar takardar mai taken "wadatar abinci a kasar Sin" kasar za ta ci gaba da taimakawa sauran kasashe masu tasowa wajen ganin sun inganta karfinsu na karkashin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da samar da ci gaba mai inganci a bangaren aikin gona na duniya.
Takardar bayanin ta kara nuna cewa, kasar Sin ta kara bude kofar kasuwar hatsinta ga kasashen waje, haka kuma, kasar Sin tana kokarin tabbatar da samar da isasshen hatsi a kasar.
Masana na cewa, matakin kasar Sin na samar da abinci, zai taka muhimmiyar rawa a yakin da ake da yunwa a duniya. (Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)