Hira da Mamane Garba daga Jamhuriyar Nijar
2019-10-23 14:24:52 CRI
A kwanakin baya ne, aka kaddamar da taron matasan Afirka da kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron matasan, taro ne dake gudana duk shekara, domin sada zumunta da kara fahimtar juna tsakanin matasan Afrika da Sin, wanda kuma daya ne daga cikin bangarorin hadin-gwiwa karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a takaice. Manufar taron ita ce, kyautatawa da raya dangantakar bangarorin biyu. Taron na kwanaki 10 na bana, ya samu halartar matasan Afirka kimanin 95 daga kasashen nahiyar 51 da kuma Tarayyar Afrika ko kuma AU a takaice. Matasan Afrika da suka halarta taron na bana, sun ziyarci birnin Beijing da wasu biranen lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, ciki har da Guangzhou, da Qingyuan da kuma Shenzhen, inda suka kara fahimtar nagartattun al'adun kasar, da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha, da kyautatuwar zaman rayuwar al'umma gami da yadda harkokin siyasa da tattalin arziki ke gudana a kasar ta Sin.
Wakiliyar sashin Hausa na CRI Fa'iza Muhammad Mustapha ta halarci wani bangare na taron a birnin Guangzhou, inda ta samu damar tattaunawa da Maman Garba dan kasar Nijar, wanda shi ne sakataren kawancen jam'iyyun kasar Nijar na Alliance Democratique pour le Niger. Kuma ya bayyana mata irin abubuwan da ya gani game da irin ci gaban da kasar Sin ta samu da kuma abubuwan da ya kamata kasarsa ta koya daga Sin. A cewarsa, gani ya kori ji, domin ya ganewa idonsa abun da yake gani a talabijin, sannan babu wani abu da bai burge shi ba, domin ya ga abubuwan da bai san su ba.(Murtala Zhang)