Ziyarar shugaba Xi a kasashen Indiya da Nepal
2019-10-17 19:24:52 CRI
Da yammacin ranar Lahadi 13 ga watan Oktoban shekarar 2019 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dawo birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, bayan ziyarar aiki da ya kai kasashen Indiya da Nepal bisa gayyatar jagororin kasashen.
Wannan ita ce ziyara ta farko da shugaba Xi ya kai zuwa ketare, tun bayan bikin cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, hakan ya bude sabon babi wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indiya da kuma Nepal.
Haka kuma ziyarar ta bude wani sabin babin karfafa alakar tattalin arziki da ciniki a yankin, da karfafa amincewa da juna da abokantaka tsakanin al'ummomin shiyyar, baya ga sabon gudummawa da ta bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar makoma a duniya baki daya.
Wannan ya shaida cewa, za a samu kyakkyawar makomar hadin gwiwa a tsakanin wadannan kasashe daga dukkan fannoni.
A bangaren Nepal, shugaba Xi, shi ne shugaban Sin na farko da ya ziyaraci Nepal tun bayan shekaru 23, kuma Nepal muhimmiyar kawar Sin ce a shawarar "Ziri daya da Hanya daya".
Ziyarar ta taimaka wajen cimma muhimman manufar hada kan kasa da kasa ta hanyar hade hanyoyin mota da jiragen kasa da kasar Nepal ta tsara ta hada da shawarar "ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar, wadanda za su taimakawa kasar Nepal wajen cimma burin samun wadata da amfanawa jama'ar kasar.
Kasashen Sin da Nepal sun amince su kara yin imani da juna a fannin siyasa. Ma'ana, kasashen biyu za su ci gaba da nuna goyon baya ga batutuwan dake shafar babbar moriyarsu, hakan zai taimakawa musu wajen yin hadin gwiwar aiwatar da manufofin samun ci gaba, da more fasahohin samun bunkasuwa, da kuma kara yin hadin gwiwa a fannoni da dama. (Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)