logo

HAUSA

Taron matasan Sin da Afirka ya baiwa matasan Afirka damar kara fahimtar ci gaban kasar Sin

2019-10-16 12:38:09 CRI

Taron matasan Sin da Afirka ya baiwa matasan Afirka damar kara fahimtar ci gaban kasar Sin

A kwanakin baya ne, aka kaddamar da taron matasan Afrika da kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron matasan, taro ne dake gudana duk shekara, domin sada zumunta da kara fahimtar juna tsakanin matasan Afrika da Sin, wanda kuma daya ne daga cikin bangarorin hadin-gwiwa karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a takaice. Manufar taron ita ce, kyautatawa da raya dangantakar bangarorin biyu. Taron na kwanaki 10 na bana, ya samu halartar matasan Afrika kimanin 95 daga kasashen nahiyar 51 da kuma Tarayyar Afrika ko kuma AU a takaice. Matasan Afrika da suka halarci taron na bana, sun ziyarci birnin Beijing da wasu biranen lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, ciki har da Guangzhou, da Qingyuan da kuma Shenzhen, inda suka kara fahimtar nagartattun al'adun kasar, da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha, da kyautatuwar zaman rayuwar al'umma gami da yadda harkokin siyasa da tattalin arziki ke gudana a kasar ta Sin. Abokan aikinmu Bello Wang da Fa'iza Muhammad Mustapha sun halarci wani bangare na taron da ya gudana a birnin Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong, inda suka yi hira da wasu matasa mahalarta taron, ciki har da wadanda suka zo daga tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Nijar. Eromosele Ehigie Daniel shi ne mataimaki na musamman na shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ya bayyana ra'ayinsa cewa, ya kamata shugabannin siyasa su bautawa al'ummar kasa. Na ga mahukuntan kauyukan kasar Sin suna nuna himma da kwazo wajen jawo hankalin masu zuba jari, da taimakawa al'ummarsu yin kere-kere da gudanar da ciniki ta Intanet, al'amarin da ya shaida cewa, gwamnatin kasar Sin na baiwa batutuwan da suka shafi jama'a muhimmanci kwarai da gaske.

Taron matasan Sin da Afirka ya baiwa matasan Afirka damar kara fahimtar ci gaban kasar Sin

Mista Eromosele Ehigie Daniel ya kuma ce, a karkashin tsarin gurguzu mai salon musamman a sabon zamanin da muke ciki, ya kalli yadda jama'ar kasar Sin ke jin dadin zaman rayuwa, gami da irin ci gaban da kasar ta samu a fannonin tattalin arziki da al'adu da ilimi gami da kimiyya da fasaha. Ya ce, shirya irin wannan taro don karfafa mu'amala da sada zumunta tsakanin matasan kasashen Afirka da na kasar Sin na da ma'ana sosai, saboda dangantakar kasar Sin da kasashen Afirka za ta ci gaba da fadada a nan gaba.

Eromosele ya ci gaba da cewa, a halin yanzu ana fama da matsalar nuna bambancin launin fata da na al'adu ko harsuna daban-daban. Amma zuwansa kasar kasar Sin a wannan karo, ya ganewa idanunsa yadda al'ummar kasar ke rungumar baki. Eromosele ya ce zai yi iyakacin kokarinsa don karfafa dankon zumunci tsakanin kasar Sin da Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya a nan gaba.

Har wa yau kuma, abokiyar aikinmu Fa'iza Mustapha ta samu damar tattaunawa da malam Adamaou Boubacar Beyaminou, dan kasar Nijar, kana mataimakin sakataren rukunin matasa na jam'iyyar PNDS-tarayya reshen Yamai, inda ya bayyana irin abubuwan da ya gani game da irin ci gaban da kasar Sin ta samu da kuma abubuwan da ya kamata kasarsa ta koya daga Sin.(Murtala Zhang)