logo

HAUSA

Taron koli na raya abota tsakanin matasan kasar Sin da na Afrika

2019-10-10 08:45:05 CRI

A ranar 27 ga watan Augustan 2019 aka bude taron matsasan Sin da Afrika karo na 4 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Manufar taron ita ce, musayar al'adu da cudanya tsakanin matasan bangarorin biyu, domin kara yaukaka zumunci da ci gaba da raya dangantakar kasar Sin da kasashen Afrika, a matsayinsu na matasa manyan gobe.

Taron koli na raya abota tsakanin matasan kasar Sin da na Afrika

Musayar al'adu da abota tsakanin matasan Sin da Afrika, daya ne daga cikin bangarorin da aka ba muhimmanci karkashin Dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC.

Yayin bude taron wanda ma'aikatar harkokin wajen Sin ta karbi bakuncinsa, mataimakin ministan ma'aikatar, Chen Xiaodong, ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha cewa, nahiyar Afrika da Sin na da makoma ta bai daya. Ya ce a bana ake cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, kuma cikin shekaru 70 da suka gabata, karkashin buri iri daya da bangarorin biyu ke da shi, an samu hanyar raya dangantaka irin ta moriyar juna. Ya ce musayar al'adu da cudanya tsakanin matasan bangarorin biyu na taka muhimmiyar rawa ga dangantakarsu, kana galibin shirye-shiryen da aka gabatar karkashin dandalin FOCAC, na mayar da hankali ne kan matasa, ta fuskar horar da su da tallafa musu. Duniya yanzu na fuskantar sauye-sauyen da aka dade ba a gani ba. Kara zurfafa dangantakar abota tsakanin Sin da Afrika, zai taimaka gaya wajen karawa kasashe masu tasowa karfi, da taimaka musu wajen bunkasa huldar kasa da kasa da tabbatar da adalci da daidaito da kuma ingiza ci gaban duniya baki daya.

Taron koli na raya abota tsakanin matasan kasar Sin da na Afrika

Dangantakar tsakanin matasan bangarorin biyu zai kara daukaka aminci da dangantakar Sin da Afrika da gina al'umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Afrika da samar da zaman lafiya da ci gaba da wayewar kan bil adama.

Taron wanda aka gudanar a birnin Beijing da kuma lardin Guangdong, ya gudana ne tsawon kwanaki 10. Kuma cikin wadannan kwanaki, matasan sun ziyarci wurare da dama da suka hada da na tarihi da al'adu da kamfanonin fasaha da garuruwan da aka raya da sauransu. Taron na bana shi ne irinsa na 4. An yi na farko ne a shekarar 2016 a nan kasar Sin, a biranen Beijing da Guangzhou, sai na biyu da aka yi a kasar Afika ta kudu, na uku kuma a lardin Sichuan na kasar Sin, sai kuma na wannan karon da aka kuma yi a birnin Beijing da lardin Guangdong.

Taron na bana da aka kammala a ranar 4 ga watan Satumba, mai taken "hada burikan matasa domin samar da dangantaka tsakanin Sin da Afrika a sabon zamani", ya samu halartar wakilai 95 daga kasashen Afrika 51, ciki har da wakilan Tarayyar Afrika AU. (Fa'iza Mustapha)