logo

HAUSA

Rumfa Sha Shirgi

2019-10-09 14:45:57 CRI

A cikin shekaru 40 da suka wuce a gundumar Hutubi, akwai wata tsohuwa dake kai dagwalo zuwa tashar sayo dagwalo. Tana ta amfani da kudin sayar da dagwalo, da kudin da ta adana don taimakawa matalauta na kabilu daban daban. Sunanta Wang Guizhen, 'yar shekaru 79 a duniya, jama'ar Hutubi suna son kiranta "Atong Khan". Kalmar da ta fito daga harshen Uygur, wadda ke nufin zuciya kamar zinari.

Gundumar Hutubi tana arewa maso tsakiyar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai. Mazauna wurin sun fito ne daga kabilu iri guda 13. Wang Guizhen 'yan kabilar Han ce ta gundumar.

Rumfa Sha Shirgi

A shekaru 60 na karnin da ya wuce, Wang Guizhen ta yi aure zuwa titin Tuanjie na unguwar Shuangqiao ta gundumar Hutubi, daga nan sai aka soma dasa irin kauna har ya yi girma.

"'Ya'ya Wang ta sha wahala sosai, tun bayan da ta yi aure, ta yi ta kula da iyayen mijinta masu fama da tashin lafiya, har zuwa rasuwar su, ba tare da yin dana sani ba."

Rumfa Sha Shirgi

A titin Tuanjie kowa ya san cewa, Wang Guizhen ta shahara ne saboda nuna kirki ga iyayen mijinta. Mazauna wurin sun kuma san cewa, Wang Guizhen ta mayar da makwabta a matsayin iyalinta.

 

Aytirahan, 'yar shekaru 83 a duniya, ta ji ciwo a kugunta a yayin da tana matashiya, har ma tana yin sunkuyo irin na digiri 90 a yayin tafiya. Mijinta ya mutu tsawon shekaru fiye da 30, kuma ba su da 'ya'ya, don haka babu wanda ke kulawa da ita. Wang Guizhen ta kan taimake ta wajen sayo kayan lambu, da dafa abinci, da yin shara, da kuma hira da ita, tana ta yin hakan na tsawon shekaru sama da 30.

"Atong Khan ta zo gida na, ta kuma kawo min kayan lambu, da burodi da kuma madara, ta kan zo don gai da ni, ni ma ina son ganinta."

Rumfa Sha Shirgi

Aytirahan ba za ta taba mantawa da wata karamar sallah ta can can da ba. Domin sanya Aytirahan ta yi biki cikin hali mai tsabta, Wang Guizhen ta wanke darduma da aka dade ba a wanke ba. Tana ta wanke dardumar sosai. Ana sanyi a watan Afirilu a jihar Xinjiang, bayan ta gama wanke dardumar, sai hannayenta suka kage ba ta iya motsa su. A yayin da take ambatar Wang Guizhen, Aytirahan ta kan ce,

"Ita ce Atong Khan, tana da zuciya ta zinari!" Amma, ba kowa ke iya fahimtar irin kaunar da Wang Guizhen ta nuna ba. Ba su fahimci me ya sa Wang Guizhen ke taimakawa sauran mutane ba, duk da ita ma na fama da talauci. Zambo da aka yi mata, da talauci da iyalinta ke fuskanta, sun taba girgiza niyyar Wang Guizhen. "Ina da 'ya'ya 7, a lokacin biyu ne kawai suka samu aikin yi. Mun sha wahala, amma na kan yi bakin ciki idan na gamu da mutane masu fama da talauci, a gani na kamata ya yi na taimake su." Chen Jiang, wadda ba ta iya ganin abubuwa masu nisa, don haka mijinta ne yake kula da ayyukan gida. Amma, a shekarar 2010, mijinta ma ya gamu da shayewar jiki sakamakon ciwo. Hakan ya sa suka shiga hali mai wuya sosai. "A lokacin, ina ji kamar sama za ta goce, ban san yaya zan yi ba. A daidai wannan lokaci, inna Wang ta kan kawo mana kayan lambu da nama, ta yi hira da ni, da karfafa min gwiwa. Na sake yin fata kan makoma."

 

A karkashin kulawa daga Wang Guizhen, Chen Jiang ta kara imani kan zaman rayuwarta. A shekarar 2014, mijinta na iya fita waje domin ya samu sauki. Chen Jiang ita ma ta soma tallafawa mutane masu bukatar taimako.

"Ina son bautawa inna Wang, zan bi inna Wang don nuna kauna ga saura." Sakamakon wannan taimakon, Wang Guizhen ta fahimci cewa, abubuwan da ta yi, hakikanin taimako ne ga sauran mutane, shi ne kuma zai iya kara imanin wani iyali kan makomarsa a nan gaba. "Ta wannan aikin tallafi, na gano cewa, abubuwan da na yi hakikanin taimako ne ga mutane, mu kuma fata ne na wani iyali mai fama da talauci. Yana da muhimmanci da ma'ana sosai, don haka ba bukatar kula da zambon da ake yi." A karkashin taimakon unguwar, Wang Guizhen ta kafa kungiyar jin kai ta "Atong Khan". A shekarar 2013, kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin na gundumar Hutubi ta kafa wa Wang Guizhen ofishin aiki na musamman.

Rumfa Sha Shirgi

Bisa kididdigar da aka yi, cikin shekaru 40, Wang Guizhen ta tallafawa tsoffi da yara sama da 240 na kabilun Uygur, Kazakh da kuma Hui, ta kuma samar da kudi da kayayyaki masu darajar RMB dubu 100.

A karkashin tasirin Wang Guizhen, diyarta ta farko Chen Hongxia ita ma ta halarci kungiyar jintai ta "Atong Khan". " Tun ina yarinya, ina ganin mama ta tana taimakawa mutane ta hanyar sayar da dagwalo, a lokacin na kan kai abinci, ko sayo kayayyaki ga mutane masu bukata. A lokacin da wadancan mutane da mama ta ta taba taimakawa suka yi mana godiya, ko suka yi mana murmushi, hakan zuciyata kan dagula. Ina alfahari da mahaifiya ta, ina son in yi koyi da ita." Henisha Mukhan, ta taba samun tallafi daga wajen Wang Guizhen a shekaru 10 da suka wuce, bayan shekaru 3 kuma, ita ma ta kasance 'yar kungiyar ta "Atong Khan". "A farko ban fahimta sosai ba, yanayin gidansu ma ba shi da kyau, me ya sa take taimakawa saura? Daga baya na soma yin aikin jin kai tare da inna Wang, sannu a hankali na gano cewa, kamata ya yi kabilu daban daban su zauna tare, suna kulawa da juna, da taimakawa juna. Idan kabilu daban daban sun hada kai, za a ji dadin zaman rayuwa." Kamar yadda Henisha Mukhan take, wadancan da suka rasa aikin yi, da mata da suka taba samun tallafi daga wajen Wang Guizhen, sun shiga kungiyar "Atong Khan" bi da bi. Kungiyar tana ta kara girma kamar garan kwallon kankara, wadda ta zama wata babbar kungiyar dake hade da kabilun Han, Uygur, Kazakh, Hui, Xibo, Kirgiz da dai sauransu da yawansu ya wuce 7000. Yanzu suna da wani suna na bai daya, wato "Atong Khan".

"Ina alfahari, cewa a cikin kungiyarmu ake ta bullo da abun koyi a fannonin taimakawa mutane, da kyautatawa ga tsoffi, da daukar matakin da ya dace, da kuma hadin kan al'umma. Jama'a sun ce, muna da zuciya mai kama da zinari, don haka ya kamata mu yi haske kamar zinari, za mu ci gaba da taimakawa mutane, don kara yada tunanin na 'Atong Khan'".