logo

HAUSA

Cikar Shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin

2019-10-03 14:55:04 CRI

Cikar Shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin

Masu hikimar magana na cewa, a kwana a tashi wata rana jariri ango ne, yau ranar 1 ga watan Oktoba na shekara ta 2019, an gudanar da kasaitaccen bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin a dandalin Tian'anmen dake cibiyar birnin Beijing, hedkwatar kasar. Haka kuma tarayyar Najeriya na murnar cikarta shekaru 59 da samun 'yancin kai daga Turawa 'yan mulkin mallaka a wannan rana. A cikin shirin Sin da Afirka na wannan mako, Ahmad Fagam da Murtala Zhang za su bayyana muku wasu manyan nasarori da ci gaban da kasar Sin ta samu a shekaru saba'in da suka gabata, gami da yadda kasar ke yin gyare-gyare a gida da fadada bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da gudummawar da Sin ta bayar ga duk duniya baki daya. Ana kuma fatan za'a kara dankon zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen dake tasowa a nan gaba, musamman kasashen Afirka, ciki har da Najeriya, Nijar, Ghana da sauransu.

Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance.(Murtala Zhang)