Ci gaban fannin wasannin kasar Sin cikin shekaru 70
2019-10-01 16:03:23 CRI
Lokacin da janhuriyar kasar Sin ke cika shekaru 70 da kafuwa, sashen Hausa na gidan radion kasar Sin CRI, na gabatarwa masu sauraro shirin musamman, game da irin manyan nasarori da kasar ta samu, da tarihi da ta kafa a fannin ci gaban harkar wasanni. A cikin wannan shiri, za mu gabatarwa mai sauraro manyan nasarori 10 da kasar ta samu cikin wadannan shekaru 70 da ke cika a bana. Jinjina ta musamman ga kasar Sin, jinjina ta musamman ga 'yan wasannin motsa jiki na kasar Sin, a gaishe ku!. 10. Chen jingkai: Dan wasan kasar Sin na farko da ya karya matsayin bajimta na duniya. Jin kadan bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, duniya ta zurawa 'yan wasan motsa jiki na Sin idanu, don ganin irin rawar da za su iya takawa a fannin gasannin kasa da kasa da ake fafatawa. Bayan shafe tsawon dan lokaci ba tare da cimma wata gagarumar nasara ba, a ranar 7 ga watan shekarar 1956, Chen jingkai ya karya matsayin bajimta na duniya, inda ya daga nauyin da ya kai kilogiram 132.5, sama da wanda takwaransa na Amurka ya daga wato kilogiram 133, yayin wata gasar sada zumunta da aka shirya tsakanin kasar Sin da tarayyar Soviet ta wancan lokaci. Bayan 'yan shekaru kuma, Chen jingkai ya sake karya matsayin bajimta har karo 9, inda shugaba MAO ya yi maraba da shi har karo 6. Chenjingkai, ya kasance dan wasan motsa jiki na kasar Sin na farko da ya ba da gagarumar gudummawa, wajen daga martabar kasar a fannin wasanni, da ma martabar Sinawa da a lokacin, yawan su ya kai miliyan 600, ya kuma yi nasarar shiga kundin tarihi, inda ake ambatar gudummawar sa, da nasarorin sa a litattafan karatu na makarantun midil, domin daliban gaba da firamare. 9. Rongguotuan: Si ne dan wasa Basine na farko da ya lashe gasar kasa da kasa. A shekarar 1959, rongguotuan ya lashe gasar kwallon tebur, ko "table tennis" a Dortmund, inda ya kasance Basine na farko da ya lashe wata gasar kasa da kasa. Shekaru 2 bayan hakan kuma, Mr. Rong da abokan wasan sa daga Sin, sun samu nasara kan tawagar kasar Japan, inda suka sake lashe kofin wannan gasa. A shekarar 1964, a matsayin sa na mai horas da 'yan wasa mata, rongguotuan ya jagoranci tawagar Sin, inda ta lashe kofin duniya ajin mata na kwallon "table tennis". Jumlar nan ta sa dake nufin "Rayuwa na tattare da koma baya, amma ban da yanzu da muka jajirce" Ta dade tana yin tasiri a zukatan Sinawa musamman matasa, wajen ingiza su su cimma manyan nasarori. Alal hakika ma dai, mutane kan kalli hoton rongguotuan, su ce wata kila shi ne mutum mafi kyawun fuska a cikin daukacin 'yan wasan motsa jiki da Sin ta taba yi. 8. xuhaifeng: Dan wasan kasar Sin na farko da ya lashe lambar zinari a gasar Olympic A shekarar 1984, xuhaifeng ya yi nasarar lashe lambar zinari a gasar wasan harba ajin maza, wannan ne karon farko da wani Basine ya samu irin wannan nasara karkashin tawagar kasar Sin. A shekarun da suka biyo baya kuma, xuhaifeng ya sake kashe lambobin zinari a gasannin nahiyar Asiya, da gasar kasa da kasa, da ma wasu gasanni na shiyya shiyya, wanda hakan ya tabbatar masa da babbar nasara a jere. 7. Tawagar mata ta kwallon volleyball ta lashe gasanni 5 a jere. Tun daga shekarar 1981 zuwa 1986, kungiyar kwallon volleyball ajin mata ta kasar Sin, ita ce ke lashe gasar cin kofin duniya, wato gasannin kasa da kasa da na Olympic, inda ta yi nasarar lashe kofunan gasannin har sau 5 a jere. Gwazon wannan kungiya ta mata Sinawa ta zaburar da matasan kasar matuka, wajen kara taka rawar gani a fannin wasanni. A gasar Olympic ta Athens da ta birnin Rio kuwa, kungiyar matan ta kasar Sin sun lashe lambobin zinari sau biyu a jere. A yanzu haka, karkashin jagorancin kocin su lang ping, kungiyar wadda ta yi nasara sau 5 a manyan gasannin kasa da kasa, tana shirin sake kafa wani tarihin samun nasarori sau 5 a jere. 6. Karbar bakuncin gasannin nahiyar Asiya ya haskaka filayen wasannin kasar Sin Daga ranar 22 ga watan Satumban shekarar 1990 zuwa 7 ga watan Oktoban shekarar, ma'aikata a birnin Beijing, suka kunna wutar yula ta wasannin Asiya. Wannan ne karon farko da Sin ta karbi bakuncin gasar kasa da kasa da ta hada nahiyoyi. Yayin wannan gasa, kasar Sin ta gwada karfin ta, na shirya gasa da ta tara 'yan wasa maasu tarin yawa. Ana iya cewa, hakan ne ya zamo mataki na aza harsashin shirin kasar na karbar bakuncin gasar Olympic ta birnin Beijing a shekarar 2008. 5. An cimma nasarar karbar bakuncin gasar Olympic ta birnin Beijing Tun a shekarar 1908 ne mujallar "tianjin youth" ta rubuta wasu manyan tambayoyi guda 3: Ta daya ita ce, shin yaushe ne kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar Olympic a karon farko?, da kuma yaushe ne Sin za ta lashe lambar zinari a karon farko a gasar Olympic? Sai kuma yaushe ne Sin za ta karbi bakuncin gasar Olympic?. A ranar 13 ga watan Yulin shekarar 2001, lokacin shugabancin Samaranch, ana bayyana birnin Beijing na kasar Sin, a matsayin wanda zai karbi bakuncin gasar Olympic na shekarar 2008. Miliyoyin Sinawa sun nuna matukar farin ciki, da dokin samun wannan dama, wadda ta zo bayan shekaru dari. Da wannan nasara Sin ta cika burin al'ummar ta, wanda a baya ba ta kai ga samun damar hakan ba. 4. A ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2001, kungiyar kwallon kafa ta maza ta kasar Sin, ta samu gurbin buga gasar cin kofin duniya. Duk da cewa lokacin ne karon farko, kuma kafin nan kungiyar ta Sin ta sha fuskantar rashin nasara a hannun kungiyoyin kasashen hadaddiyar daular larabawa da kasar Qatar, amma a shekarar 2001, kungiyar Sin ta halarci gasar cin kofin duniya bayan ta doke Qatar, da hadaddiyar daular larabawa, kaza lika ta samu nasara kan Oman da ci 1 da nema, a wasannin neman gurbi na rukunin kasashen Asiya, wanda aka buga gabanin gasar ta cin kofin duniya. Duk da tarin kalubale da ta fuskanta, tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Sin ta ciri tuta, wajen kaiwa ga buga gasar cin kofin kwallon kafa ajin maza na kasa da kasa. 3. Gasar Olympic ta Beijing ta 2008: ma'aunin babbar nasarar da Sin ta cimma A shekara ta 2008 ne birnin Beijing ya karbi bakuncin gasar Olympic, inda tawagar kasar Sin ta lashe lambobin yabo har guda 100, matakin da ya nuna cewa, kasar ta yi gaba da yawan lambobin yabo a gasar. Sama da kasashe da yankuna 200 ne suka halarci gasar ta birnin Beijing. Har bayan shekaru 10 da gudanar wannan gasa, gasar Olympic ta birnin Beijing na cikin zukatan al'umma, inda ta kasance gasa mafi samun cikakkiyar nasara, a jerin gasannin Olympic da aka taba gudanarwa a tarihi. 2. Sin ta lashe kofin gabashin Asiya na shekarar 2010, bayan ta doke koriya ta kudu A cikin shekaru 32, wato tun daga shekarar 1978 zuwa shekarar 2010, tawagar kwallon kafa ta kasar Sin ta maza, ba ta taba yin rashin nasara a hannun takwararta ta koriya ta kudu ba. Nasarorin da Sin ta samu kan Koriyar cikin shekaru 32, sun yi daidai da yawan shekarun fara aiwatar da manufofin gyare gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. A shekarar 2010, Sin ta lashe wasan ta da koriya ta kudu da ci 3 da nema, a gasar kasashen gabashin Asiya, nasarar da ta daga darajar kungiyar a fannin taka leda, musamman kasancewar a wannan wasan ne dan wasan Sin dengzhuoxiang ya taka muhimmiyar rawa, ya kuma zura kwallo mafi ban sha'awa da kungiyar kwallon kafar kasar ta taba zurawa a raga. 1. An sake sanya dan ba a sabon burin neman "Lashe gasanni 5 a jere " A gabar da lang ping ke rike da ragamar kungiyar kwallon "volleyball" ta kasar Sin tun daga shekarar 2014, kungiyar mata mai bugawa Sin wannan kwallo, na shirin lashe gasar kasa da kasa karo na 5 a jere. Wannan kungiya wadda ta lashe gasar duniya ta birnin Rio a karon farko ta kuma yi nasara, ta lashe wasanta da daya daga kungiyoyin hamayya da ci 3 da nema. Nan gaba dai, akwai hasashen ganin wannan kungiya ta cimma wannan buri na lashe gasar kasa da kasa sau 5 a jere. Lallai wannan kungiya ta gamu da sa'a ta samun wadannan nasarori. Daukakar fannin wasanni a kasar Sin, na alamta irin ci gaba da kasar ke samu, da kuma nasarori masu tarin yawa da 'yan wasan ta ke samu.
Yayin da janhuriyar jama'ar kasar Sin ke ciki wadannan shekaru 70, ba bu abun fata illa samun karin ci gaba, da wadata mai dorewa, da kuma farin ciki da annashuwa!(Saminu, Amina Xu)