logo

HAUSA

Sin ta samu gagarumin ci gaba a fannin raya wasannin Olympics cikin shekaru 70 da kafuwar sabuwar jamhuriyar kasar

2019-09-27 16:55:04 CRI

Alal hakika duniya ta ganewa idanun ta irin gagarumin ci gaba da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki, da zamantakewar al'umma tun daga shekarar 1949 wato shekaru 70 da suka gabata; tun kafuwar sabuwar janhuriyar kasar Sin kawo yanzu. Cikin wadannan shekaru, tattalin arzikin kasar Sin ya yi matukar fadada daga dukkanin fannoni, yayin da karfin sa ke kara yin tasiri ga tattalin arzikin duniya baki daya. Sin ta yi namijin korari wajen aiwatar da matakan bunkasa kan ta a sassa daban daban, ciki hadda fannin ilimi, da kiwon lafiya, da raya masana'antu, da kirkire kirkire. Sauran sun hada da kiyaye muhalli da raya harkokin wasanni da dai sauran su. Masharhanta da dama na bayyana cewa, matakan da Sin ke aiwatarwa na sauye sauye a gida, da bude kofa ga kasashen waje ya sha banban da na sauran kasashe. Wato dai Sin na bin wani salo ne na bi sannu, bisa yanayi da ya dace da yanayin zamantakewar al'ummar ta, da kuma manufofi sihihai dake tsare cikin kudurorin JKS na raya kasa, matakan da suka fara yaduwa tun daga raya fannin noma, da rage gibin dake tsakanin birane da yankunan karkara. Ko shakka ba bu banbancin dake tsakanin kasashe masu ci gaba da masu tasowa yana da nasaba da gibin dake tsakanin ilimi da kuma albarkatu. Sin ta lura da wannan lamari, wanda ya sanya ta zuba jari mai tarin yawa a fannin raya Ilimi, ta kuma tsaya tsayin daka wajen fadada ayyukan kirkire kirkire da koyo da koyarwa, ta kuma yi kokarin wajen raya harkokin cinikayya da zuba jari a waje, ta kuma yi koyi daga kwarewar sauran sassan duniya. A fannin wasanni, bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ya sanya al'ummar Sinawa samun zarafi na inganta kiwon lafiyar su, ciki hadda raya fannin wasanni wanda muhimmin ginshiki ne na kula da lafiya, da samar da nishadi ga bil Adama. Gwamnatin Sin ta dora muhimmancin gaske ga raya fannin wasanni, ta kuma shiga an dama da ita a gasannin kasa da kasa, matakin da ya kai ta ga karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin zafi a shekarar 2008. A ranar 13 watan Yulin shekarar 2001, kwamitin hukumar wasannin Olympic na kasa da kasa ko IOC, ya bayyana birnin Beijing, a matsayin wanda zai karbi bakuncin gasar ta 2008, wanda hakan ya sanya Sin shiga jerin kasashen duniya dake taka rawar gani a fannin karbar bakuncin gasannin kasa da kasa. Kamar yadda gasannin Olympics na birnin Tokyo a shekarar 1964, da ta birnin Seoul a shekarar 1988 suka daga darajar kasashen Japan da Koriya ta Kudu, a matsayi na kasa da kasa, ita ma gasar Olympics ta birnin Beijing ta zamo fitila da ta kara haska kasar Sin, ta kuma nuna irin ci gaban tattalin arziki da kasar ta samu, da ma tasirin ta ta fuskar siyasa. Hakan ya yi daidai da fahimtar tsoho firaministan Sin Wen Jiabao, wanda a ranar 24 ga watan Afirilun shekarar 2008, ya ce gasar Olympics ta birnin Beijing, ta gabatarwa Sin wata dama ta nunawa duniya irin salon ta na mulkin kai, da bude kofa, da wayewar kai, da martaba abokantaka, da zaman jituwa da sauran sassa. Bisa alkaluman kididdiga, gasar Olympics ta birnin Beijing ta shekarar 2008, na cikin mafiya tsada da aka taba gudanarwa, inda cikin kwanakin gasar 16, wato tsakanin ranar 8 ga watan Agusta zuwa 24 ga watan, aka gudanar da rukunin wasanni 28 a zaurukan wasanni 37, aka kuma lashe kambobin gasar har 302. Bugu da kari birnin Beijing, da wasu karin biranen ciki hadda Hong Kong; da Qingdao, da Shandong; Qinhuangdao, da Hebei; da Shanghai; da Shenyang, da Liaoning; da Tianjin suka karbi bakuncin wasannin na Olympics. Kafin gudanar gasar ta Olympics a shekarar 2008, Sin ta fitar da taken gasar da za ta karbi bakunci, wanda shi ne "Duniya daya, mafarki daya," wanda aka yi amfani da shi wajen yayata manufar kiyaye muhalli da amfani da fasahohin zamani wajen gudanar da gasar Olympics. Domin tinkarar wannan gasa, Sin ta zuba jarin da yawan sa ya kai dalar Amurka kusan biliyan 40 tsakanin shekaru 2002 zuwa 2006, inda ta sauya fasalin birnin Beijing, domin ya dace da yanayin karbar bakuncin wannan shahararriyar gasa. Ko shakka babu daga karshe kwalliya ta biya kudin sabulu, inda baya ga nasarar da aka samu ta kammala gasar cikin nasara, Sin ta lashe lambobin zinari ta wasanni da 'yan kasar suka shiga a matakai daban daban. Cikin fitattun 'yan wasan kasar da suka taka rawar gani akwai Liu Xiang, wanda ya lashe lambar zinari a wasan gudu da tsallake shinge, da dan wasan linkaya Guo Jingjing wanda shi ma ya lashe lambar zinari a wannan fage. A bangaren raya tattalin arziki kuwa, gasar Olympics ta birnin Beijing ta yi matukar tasiri wajen bunkasar hada hadar cinikayya, da raya muhalli. Kaza lika sauran fannoni da suka samu tagomashi sakamakon gasar sun hada da fannin tallace tallace, da ayyukan yada bayanai ta kafofin talabijin, da yanar gizo, da yawar salula, da amfani da makamashi mai tsafta, da sauran sassa na wasanni. Gina sabon birnin Beijing Bayan samun amincewar birnin Beijing ya karbi bakuncin gasar Olympics ta 2008, Sin ta fara aikin shiri na shekaru 7 domin cimma matsayi da hukumar shirya gasar Olympics ta IOC ke bugata ga kasa mai karbar bakuncin wannan babbar gasa. Bayan nazartar gasannin da suka gabata a biranen Sydney da Atlanta, kwamitin hukumar da aka dorawa nauyin shirya wannan gasa ta Beijing ko BOCOG a takaice, ya dukufa wajen samar da kayayyaki da ake bukata domin wannan babbar gasa. Domin hade ayyukan hukumomin gwamnatin tsakiya, da na hukumar birnin Beijing, da kuma kwamitin shirya gasar ko BOCOG waje guda, Gwamnatin Sin ta kafa wata tawagar aiki ta musamman wadda a wancan lokaci mataimakin firaministan Sin Li Lanqing ya jagoranta, tare da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar, domin tabbatar da nasarar shirin da aka tsara. A cewar Mr. Michael Payne, wanda ya yi aiki da IOC tsawon sama da shekaru 20, Sin ta lura da muhimmancin hade sassan ayyukan IOC, da BOCOG, da kuma birnin da zai karbi bakuncin gasar Olympics. Bayan nazartar dabarun kasashen da a baya suka cimma nasarar karbar bakuncin gasar, sai aka debo ma'aikatan BOCOG daga jami'an gwamnatin birnin Beijing, da kwararru daga hukumar kwallon kafar kasar, kana aka damka jagoranci hannun babban sakataren JKS na birnin Beijing Mr. Liu Qi, da mataimakin shugaban kasa Wang Qishan, wanda a lokacin shi ne magajin garin birnin. Wajen aiwatarwa bisa tsarin da aka tanada, birnin Beijing ya yi matukar kokarin kaiwa matsayi na kasa da kasa, tare da kaucewa rashin bin ka'ida. Cikin muhimman sassa da aka zubawa jari yayin da ake wannan aiki akwai fannin samar da kayan wasa.