Hadin gwiwar kasashen Sin da Najeriya
2019-09-26 15:47:22 CRI
Tun lokacin da kasashen Sin da Najeriya suka kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu a ranar 10 ga watan Fabarairun shekarar 1971, dangantakar kasashen take ta kara bunkasa, har ma suka fadada alakar zuwa fannoni daban-daban. Kafin kulla wannan alaka, jami'an kasashen biyu sun sha ziyartar kasashen juna a mabanbantan lokuta.
Najeriya dai ita ce, kasa mafi yawan al'umma da ma karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, yayin da kasar Sin ke zama babbar kasa mai tasowa mafi yawan al'umma kana ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Yanzu haka, kasashen Sin da Najeriya na alaka a fannonin aikin gona, da al'adu, ilimi, da kafofin watsa labarai, mata da matasa, harkokin cinikayya da sauransu.
Yayin da kasashen ke raya alaka a tsakaninsu, sun kuma yi alkawarin kare manufofi da muradun juna da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan juna da goyon bayan juna a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya da makamantansu.
Bugu da kari, sassan biyu sun lashi takwabin karfafa tuntubar juna don tabbatar da ganin an aiwatar da sakamakon da aka samu yayin taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) da shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)