logo

HAUSA

Matsayin matan kasar Sin a fannin siyasa ya karu sosai, sun kuma samu tabbaci a fannin kiwon lafiya da samun ilmi

2019-09-26 18:25:23 CRI

A makon da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken "Daidaito, ci gaba da amfana tare: Ci gaban gwagwarmayar mata a cikin shekaru 70, bayan kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin". Inda aka nuna cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, a yayin da kasar Sin ke neman ci gaba yayin da take tasowa, zuwa lokacin da ta samu wadata da kuma karfi, sha'anin mata ma ya samu gagarumar nasara a tarihin kasar. Ya zuwa yanzu, matsayin matan kasar Sin a fannin siyasa ya karu sosai, kuma an ba su tabbaci sosai a fannonin kiwon lafiya da samun ilmi. Ana iya cewa, matan kasar na kara taka muhimmiyar rawa a fannin rayuwar al'umma, kana suna kara samun alheri.  A cikin takardar bayanin da aka fitar a wannan rana, an nuna cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci kan tabbatar da daidaito a fannin harkokin siyasa a tsakanin mata da maza. A lokacin da aka fara kafa sabuwar kasar Sin, an kafa dokokin cewa, maza da mata daidai su ke a fannonin 'yancin yin zabe da zabarsu, da kuma ikon gudanar da harkokin kasa. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, a yunkurin zamanintar da tsarin tafiyar da harkokin kasa bisa doka, matsayin mata na tafiyar da harkokin kasa da na al'umma ya karu a dukkan fannoni. Bisa alkaluman da aka samu a shekarar da ta wuce, a cikin jami'ai na hukumomin gwamnati na kasar Sin baki daya, yawan mata ya kai kaso 22.2, kana yawan wakilai mata a babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 ya kai kusan kashi 1 cikin 4. Ban da wannan kuma, ana damawa da mata a ayyukan gudanar da harkokin demokuradiyya a kananan hukumomi. A shekarar 2017, yawan mata dake zaunannun kwamitoci ya kai kusan kaso 50. Mataimakiyar darektar kwamitin kula da harkokin mata da yara ta majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma mataimakinyar shugabar hadaddiyar kungiyar mata ta kasar, malama Huang Xiaowei ta bayyana cewa, a cikin shekaru 70 da suka wuce, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana nacewa kan manufar zaman daidaito a tsakanin maza da mata, da ba da muhimmanci ga tabbatar da 'yancin mata da zaman daidai wadaida a tsakanin maza da mata, da kara yin kirkire-kirkire da kyautata tsarin dokoki da ayyukan kare hakkin mata. Huang Xiaowei ta ce, "Yanzu an bullo da wani tsarin dokoki na kiyaye 'yanci da moriyar mata kamar yadda tsarin mulki ya tanada, da mai da hankali kan dokar kare 'yanci da moriyar mata, wanda ya kunshi dokoki da ka'idoji sama da 100, hakan ya samar da abubuwa shaida kan yadda ake kare 'yanci da moriyar mata sosai. Ya zuwa shekarar 2018, larduna da birane guda 30 na kasar Sin sun bullo da tsarin kyautata zaman daidaito a tsakanin maza da mata bisa dokoki, hakan ya tabbatar da ra'ayin zaman daidai wadaida a tsakanin maza da mata ta fannonin tsarawa da gudanarwa da kuma sa ido kan dokoki." A cikin shekaru 70 da suka gabata, tabbatar da matsayi da hakkin mata na kasar Sin, ya taimaka musu wajen bunkasa zamantakewar al'ummar kasar. A halin yanzu, ana samun mata fiye da 4 cikin 10 dake aiki a dukkan sana'o'i. 'Yar sama jannati ta farko ta kasar Sin Liu Yang, da kwararriyar farko ta Sin da ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel Tu Youyou, da kuma mata 8 dake cikin jerin sunayen mutane 42 da suka samu lambobin yabo na kasar Sin, dukkansu sun shaida cewa, mata sun ba da gudummawa wajen ci gaban kasar Sin. Marigayi tsohon shugaban kasar Sin Mao Tsedong ya taba yabawa matan kasar Sin cewa, suna taka muhimmiyar rawa a zamantakewar al'ummar kasar. Rahoton da cibiyar bincike ta McKinsey ya fitar a shekarar 2017, ya nuna cewa, yawan GDP da mata ke samarwa a kasar Sin ya kai kashi 41 cikin dari, wanda ya zama matsayin koli a dukkan yankunan duniya. Baya ga haka, takardar bayanin ta ce, lafiyar mata da kananan yara shi ne ginshikin kiwon lafiyar al'umma baki daya. Gwamnatin kasar Sin tana mayar da hankali sosai kan ayyukan kiwon lafiyar mata da yara, inda ta sanya wannan fanni a cikin manyan tsare-tsare na kasa, tare kuma da kara kyautata tsarin dokoki na kiyaye lafiyar mata da kananan yara. Bayanai na cewa, tun bayan da kasar Sin ta soma gudanar da ayyukan bincike kan cutar sankarar mama da sankarar mahaifa ga matan dake kauyuka, ya zuwa yanzu, an yiwa mata sama da miliyan 85 bincike mai nagarta kan cutar sankarar mahaifa, da binciken sankarar mama ga mata sama da miliyan 20, ban da wannan kuma, an ba da tallafin jinya ga mata masu fama da cutar sankara dake fama da talauci ko samun kudin shiga kadan. Mataimakiyar shugabar hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin Tan Lin ta bayyana cewa, ita ma kasar Sin ta kara samar da hidimar kiwon lafiyar jama'a ga mata da yara, da kara inganta ayyukan kiwon lafiyar mata a matakai daban daban na rayuwarsu. Tan ta ce, "Tun bayan da aka soma gudanar da tsarin haihuwar 'yaya biyu, kasar Sin ta karfafa ba da hidimar kiwon lafiya ga mata a yayin da suka samu juna biyu a dukkan fannoni. Ciki har da kafa sashen ba da shawarwarin lafiya ga mata kafin samun ciki, da binciken lafiyar uwa kafin haihuwa, da kuma samar da hidimar sa ido ga matan da aka sallamesu daga asibiti bayan sun haihu da binciken lafiyarsu har tsawon kwanaki 42 bayan samun juna biyu, da duba lafiyar mata masu juna biyu a kowane mako da bayan kwanaki 42 bayan sun haihu. Ban da wannan kuma, kasarmu ta bullo da wurin samar da jinya na lokacin balaga da na sakin kwan halittar biladama a hukumomin kiwon lafiyar mata da yara, hakan za a sanya matan dake matakan rayuwa daban daban samun hidimar lafiya yadda ya kamata." Alkaluman da aka samu na nuna cewa, yawan matan dake da karancin ilmi masu sama da shekaru 15 a kasar Sin, ya ragu daga kashi 90 cikin 100 kafin kafuwar sabuwar kasar Sin zuwa kashi 7.3 cikin 100 a shekarar 2017, lallai an samu babban sauyi. Manufar ba da ilmin tilas na shekaru 9 ta taimaka wajen kawar da banbanci a tsakanin maza da mata a nan kasar Sin. Mataimakiyar shugabar hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin, malama Meng Man ta ce, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan 'yancin samun ilmi ga yara mata ta hanyar matakan rage yawan matan dake da karancin ilmi, Ta ce,

"Tsarin mulkin kasa ko kuma dokar ba da hidimar tilas, dukkansu sun kayyade cewa, yara mata na samun daidaito kan 'yancin samun ilmi. Baya ga haka, dokar ta ba da tabbacin 'yanci da moriyar mata, sannan ita ma ta bukaci cewa, dole ne iyaye ko kuma masu riko su dauki nauyinsu na ba da tabbaci ga yara mata wajen cin gajiyar tsarin samun ilmi tilas. Ya zuwa shekarar 2017, yara mata da suka shiga makaranta ya kai kashi 99.9 cikin 100, adadin da ya yi daidai da yara maza. Ga misali, dalibai mata dake karatu a jami'o'i sun kai kashi 52.5 cikin 100, wanda ya wuce adadin dalibai maza."(Bilkisu)