Nasarorin kasar Sin cikin shekaru 70 da suka gabata
2019-09-19 14:29:34 CRI
A ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa ne, za a gudanar da bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a dandalin Tian'anmen dake birnin Beijing, hedkwatar kasar. Ana fatan a yayin bikin, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar, kana shugaban kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kolin sojin kasar, Mista Xi Jinping, zai gabatar da muhimmin jawabi.
Sannan bayan bikin, za a shirya faretin sojoji da sauran shagulgula domin murnar wannan muhimmiyar rana. Haka kuma a wannan rana,shugaba Xi Jinping zai ba da lambobin yabo da na girmamawa na kasa ga fitattun mutanen da al'ummar kasar suka amince da gudunmawa da suka ba da a fannonin raya ci gaban kasa da tsaron kasar mai tsarin gurguzu, da kuma 'yan kasashen waje da suka bada babbar gudunmawa a fannin raya kasar Sin, da ingiza hadin gwiwar kasar Sin da kasashen ketare, da ma kiyaye zaman lafiyar duniya, haka zalika da fitattun mutanen da suka bada babbar gudummawa a sana'o'insu daban daban, wadanda kuma suke da kima a tsakanin al'umma..
Duk masu bibbiyar yadda al'amurra ke wakana game da irin manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma ta fuskar raya ci gaban tattalin arzikinta, da inganta yanayin zaman rayuwar al'ummar Sinawa, da tsaron kasa, da kyautata matsayin tsarin gurguzu mai sigar musamman a sabon zamanin da muke ciki, da raya manyan fasahohin zamani, da kyautata manufofin kasar na yin gyare gyare a gida da bude kofarta ga waje, musamman wajen kara zurfafa mu'amalar diflomasiyya da kasa da kasa, da bada babbar gundummawa wajen wanzar da zaman lafiyar kasa da kasa na MDD, da hadin gwiwar kasar Sin da kasa da kasa karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya", kana da zurfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Asiya, da bada gudunmawa wajen bunkasa cigaban kasashe masu tasowa musamman kasashen nahiyar Afrika karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC
Wadannan nasarorin sun kara fito da matsayin kasar Sin a idanun duniya a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Ya kamata kasa da kasa su yi nazari kan manufofin da kasar Sin ta aiwatar tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin shekaru 70 da suka gabata wajen gina al'ummar Sinawa da bada babbar gudunmmawa ga al'ummar duniya da nufin kyautata makomar bil adama don a gudu tare a tsira tare. (Saminu, Ahmad, Ibrahim/Sanusi Chen)