logo

HAUSA

PSG: An janye dakatarwar da aka yi wa Neymar

2019-09-19 15:24:32 CRI

Neymar ya so barin PSG a kakar wasa ta bana amma hakan bai samu ba

Kotun sauraron kararrakin wasanni ta janye dakatarwa guda daga cikin uku da aka yi wa dan wasan gaban Paris St-Germain Neymar.

Hukumar shirya gasar Zakarun Turai ce dai ta dakatar da Neymar buga wasa uku sakamakon cin zarafin wasu alkalan wasa.

An dakatar da Neymar mai shekara 27 ne biyo bayan karawar kungiyarsa ta PSG da Manchester United a wasan da PSG din ta sha kashi da 1-3 a filin wasa na Old Trafford.

A ranar shida ga watan Maris ne Man Unitedta ta karbi bakuncin PSG a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League bayan PSG ta ci wasan farko a Faransa.

Dan wasan ya kira finaretin da aka bai wa United a zagaye na biyu na wasan a matsayin abin kunya.

Matakin da UEFA ta dauka ya sanya Neymar ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Real Madrid da Galatasaray ba.

Sai dai zai taka-leda a ranar 22 ga watan Oktoba a wasansu da Club Brugge a Champions League.

Champions League: Messi zai buga wasa a yau

David De Gea ya sabunta kwantaraginsa da Man United

Rashin amincewa da matakin na UEFA ya sanya PSG mika korafi gaban kotun, bayan da tun farko ta bukaci da a yi wa dan wasan sassauci.

Kotun kafin yanke hukuncin ta bayyana cewa sai ta binciko dalilan da suka sanya aka yanke hukuncin dakatar da Neymar cikin 'yan makonni.

A wancan lokacin Neymar na fama da jinya, lamarin da ya sanya bai samu damar halartar wasannin da kungiyarsa ta fafata da Man United ba.

Bayan da alkalin wasa Damir Skomina ya sake nanata kallon bidiyon yadda kwallon da Diogo Dalot ya buga ta daki hannun dan wasan bayan PSG Presnel Kimpembe ne ya yanke shawarar bai wa United din damar bugun kwana.

Finaretin da Marcus Rashford ya ci shi ne ya bai wa United din nasara, inda suka tashi wasan 3-1. Hakan ya sanya PSG ta gaza tsallakawa zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar Champions Laeague.

Neymar ya sanya a shafinsa na sada zumunta cewa: "Wannan abin kunya ne. A ce mutum hudu da ba su san komai a harkar kwallon kafa ba su ne za su yanke hukunci a gaban talabijin. Ta ya ya za a yi ya busa finareti bayan bai gani ba."