logo

HAUSA

Yadda "Iyalin Anqi" ke kokarin taimakawa yara masu fama da lalurar kwakwalwa

2019-09-19 20:33:13 CRI

Yadda "Iyalin Anqi" ke kokarin taimakawa yara masu fama da lalurar kwakwalwa

Babbar diyar Wang Fang, wadda ta kafa hukumar ta "Iyalin Anqi", ta kamu da matsalar kwakwalwa a shekarar 2002, a yayin da take jinyar diyarta, ta tsaida kudurin cewa, za ta kafa cibiyar taimakawa yara masu fama da matsalar kwakwalwa, wannan ya sa ta kafa cibiyar "Iyalin Anqi" farko a garinsu wato birnin Nanning na lardin Guangxi dake kudu maso gabashin kasar Sin, domin taimakawa yara da yawa dake fama da wannan lalura, a wani filin da fadinsa bai kai muraba'in mita 50 ba. Shugaban cibiyar Wang Fang ta gayawa wakilinmu cewa, ba kawai "Iyalin Anqi" yana kula da yara masu fama da matsalar kwakwalwa ta hanyoyi daban daban ba, abun mafi muhimmanci shi ne, taimakawa wadannan yara ta yadda za su dawo cikin al'umma, har ma su kasance masu muhimmanci ga al'umma a nan gaba. Wang Fang ta bayyana cewa, "Yara masu fama da matsalar kwakwalwa da yawa ne suke zaune da ma samun jinya a asibiti da kuma cibiyar tun suna kanana. Na kan ce, yaya wadannan yara za su yi a nan gaba? Ina ganin, ya kamata a samu wurin da za a taimaka musu su samu sauki, su samu ilmi kamar sauran yara, ta yadda za su samu ci gaba a dukkan fannoni. Tun lokacin da muka kafa cibiyar zuwa yanzu, ko da yaushe muna bunkasa 'Iyalin Anqi' a fannoni guda biyu. Da farko shi ne, kara kwarewar yaran a fannin fasaha, da fannin da kowanne yaro ya fi kwarewa. Na biyu shi ne, muna kokarin shirya ayyuka iri daban daban ta yadda jama'a za su kara fahimta da ma sanin matsalar da wadannan yara ke fama da ita, saboda burinmu shi ne, taimakawa mutane masu wannan matsala su dawo cikin al'umma ba tare da wata matsala ba."

Yadda "Iyalin Anqi" ke kokarin taimakawa yara masu fama da lalurar kwakwalwa

 

Da farko, "Iyalin Anqi" yana samar da hidima ne ga yaran dake tsakanin shekaru 3 zuwa 15. Amma, ya zuwa yanzu, wannan cibiya da aka kafa shekaru 17 da suka gabata, tana ta habaka fannonin hidima da abubuwan hidima, har ma ta kafa makarantu guda uku, ciki har da cibiyar ci gaban yara, cibiyar ci gaban matasa da ta ba da hidima ta al'umma. Wang Fang ta ce,

"Yanzu yara 'yan kasa da shekaru 12 ba za su rika kwana a cibiyar ba. Saboda bayan binciken da muka yi na wasu shekaru, mun gano cewa, kamata ya yi kananan yara su kasance tare da iyalinsu. Don haka, muka soma raya cibiyar matasa, inda wadanda shekarunsu suka wuce 16 za su rika kwana a cibiyar. Ban da wannan kuma, a shekarar 2016, mun soma ba da hidima ga marayu, domin ganin wadannan ayyukan sun gudana yadda ya kamata, mun hada kai da hukumar kula da harkokin jama'a, don kafa cibiyar samar da alheri ga jama'a, inda muka fadada ayyukanmu zuwa na ba da hidima ga marayu da yara marasa galibu."

 

Ya zuwa shekarar 2019, "Iyalin Anqi" ya samar da taimako da hidima ga yara sama da dubu biyu. A lokaci guda kuma, cibiyar ta hada kai da wasu hukumomi abokan hulda masu zaman kansu na kasar Sin wadanda yawansu ya kai kimanin 60, kana a ko wace shekara tana samar da horo a fannonin fasahar kula da masu irin wannan matsala, da ba da ilmi na musamman, da kara kwarewar ma'aikatan al'umma da hukumomin da abun ya shafa na wurare daban daban na kasar. "Iyalin mahaifiya" dake birnin Kashgar na jihar Xinjiang yana daya daga cikin hukumomin.

Yadda "Iyalin Anqi" ke kokarin taimakawa yara masu fama da lalurar kwakwalwa

 

A watan Mayu na shekarar 2013, bayan samun horo a "Iyalin Anqi", sai Ayinur Halik, daga birnin Kashgar ta kafa wata cibiya mai suna "Iyalin mahaifiya" a garinsu karkashin jagorancin Wang Fang. Ayinur ta ce, tana fatan kafa iyali mai kaunar yara masu bukatun musamman kamar "Iyalin Anqi". Ta bayyana cewa,

"Tun lokacin da muka kafa 'Iyalin mahaifiya' zuwa yanzu, mun ba da taimako ga yara masu fama da lalurar kwakwalwa masu shekaru 3 zuwa 14, wadanda suka fito daga iyalin da miji shi kadai ko mata ita kadai ke lura da yara, kuma ke fama da talauci. Wadannan yara ba za su biya ko kobo ba, ya zuwa yanzu yaran da suka ci gajiyar tallafin cibiyar mu sun wuce dubu daya. Ana iya cewa, madam Wang Fang ita ce mahaifiyar dukkan yara masu fama da lalurar kwakwalwa dake birnin Kashgar." Shugabar "Iyalin Anqi" Wang Wang ta ce, lokacin da ta fara kafa cibiyar ta tsara wani shiri na tsawon shekaru goma, wato a shekaru biyu na farko za a kara habaka fannonin ba da hidima, za kuma a kafa wata kungiya ta fasaha. A cikin shekaru biyar masu zuwa kuma, za a koyar da sauran hukumomi masu irin wannan aiki ta yadda za su ci gajiya. A shekarar 2018, "Iyalin Anqi" shi ne na farko da ya lashe gasar yin kirkire-kirkire ta kasa da kasa mai suna "We Work" da aka shirya a birnin Los Angeles na kasar Amurka, inda cibiyar ta samu kyautar RMB kusan dubu 127, a cewar Wang Fang, za a yi amfani da wadannan kudade ne don raya cibiyarta a cikin shekaru biyu masu zuwa. Ta ce,

"Bisa shirin da muka tsara, nan gaba za mu yi amfani da wadannan kudade don kafa wata makaranta da gidan kula da yara. Ban da wannan kuma, wasu matasa masu fama da matsalar kwakwalwa suna fuskantar matsalar samun aikin yi, don haka muna fatan kara karfinmu na koya musu sana'a ta yadda za su dagara da kansu. Game da wadancan matasan da har yanzu ba su shiga cikin al'umma ba, za mu yi kokarin samar musu wani gida da za su zauna ta yadda za su kare mutuncinsu. "(Bilkisu)