logo

HAUSA

Matakan kasan Sin na kare kayayyakin tarihi

2019-09-05 18:04:57 CRI

Masana na bayyana al'ada a a matsayin madubin al'umma, abin da ke nunawa 'yan baya irin rawar da magabantansu suka taka wajen kare kayayyakin al'adu dana tarihi masu muhimmici na tsawon dubban shekaru. Wannan ya sa a kwanakin baya, shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya bukaci masana da kwararru, da su kara azama wajen kare kayayykin tarihi da na al'adun kasar.

Matakan kasan Sin na kare kayayyakin tarihi

Xi Jinping ya yi wannan kira ne, yayin taron musayar ra'ayi da ya gudana a garin Dunhuang dake lardin Gansu, inda ya bukaci masana da wakilain sassan hukumomin raya al'adu, da su himmatu wajen cimma wannan muhimmin buri.

Bugu da kari, shugaban na kasar Sin, ya jaddada muhimmancin hada gwiwar bunkasawa, da yayata al'adun gargajiyar kasar Sin. Kaza lika ya yi kira da a kara azama, wajen aiwatar da musayar tsakanin kasar sa da sauran kasashen duniya, a kuma yi koyi da managartan nasarorin da sauran kasashe, da yankunan duniya suka cimma.

Matakan kasan Sin na kare kayayyakin tarihi

Kasar Sin na da wurare da kayayyakin tarihi masu tarin yawa da hukumar UNESCO ta amince da su. Irin wadannan wurare da kayayyaki sun taimaka wajen nuna wayewar kan kasar Sin na dubban daruruwan shekaru.

Masu fashin baki na cewa, irin wadannan kayayyakin tarihi, suke nuna basiri da hikima wanda ke kunshe da tsarin rayuwa ta fannonin abinci da sutura da tsaro da sauransu na al'ummomin da suka gabata. Don haka, kare su na da muhimmaci matuka. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)