logo

HAUSA

Amina Tahir Maude(I)

2019-09-03 09:54:19 CRI

A kwanakin baya ne, dalibai 'yan Najeriya 58 suka samu kudin tallafin karatu da gwamnatin kasar Sin ta samar, inda za su fara karatu a fannonin injiniya, likitanci, ayyukan gona da dai sauransu daga wannan watan Satumba da muke ciki domin kokarin neman samun digiri na farko da na biyu da kuma na digirgir. A halin yanzu, Sin da Najeriya na hadin gwiwa sosai a fannoni daban daban ciki har da samar da ilmi. Yanzu yawan dalibai 'yan Najeriya da ke kara ilmin a kasar Sin ya zarce 6000, 500 daga cikinsu sun samu kudin tallafin karatu da Sin ta samar musu. Shirin "In Ba Ku Ba Gida" na yau na farin cikin gabatar muku da wata bakuwa mai suna Amina Tahir Maude. Amina daya ce daga cikin wadancan dalibai 6000 da ke kara ilmi a nan kasar Sin.

A zantawarta da wakiliyarmu Fa'iza Mustapha, Amina ta yi mana bayani kan yadda take karatu da zama a nan kasar Sin, kuma ta yi kira ga Hausawa mata da su tashi domin samun abun dogoro da kai.(Kande Gao)