logo

HAUSA

Wasan kwallon kwandon yana sharewa 'yan mata hanyar fita daga yanki mai tsaunuka

2019-08-29 17:28:14 CRI

Da yammacin wani lokaci na yanayin zafi, wasu yara mata su uku suna gwajin wasan kwallon Kwando a filin wasa, yayin da gumi dake fuskokinsu yake cigaba da zuba a kasa. Basu damu da yanayin zafin ba, Yao Xiaoni, yar kimanin shekaru 13 da haihuwa, daya daga cikin 'yan matan uku dake yin wasan daga yankin arewacin kasar Sin mai fama da talauci wato yankin Taiyue mai tsaunuka, tana matukar jin dadin wasannin. "Ba abu ne mai sauki ba samun damar fita daga yanki mai tsauni," Yao ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yayin da take fama da wasan kwallo a makarantar Middle School ta Jinshan dake birnin Taiyuan, na lardin Shanxi. A wancan lokacin, wasan kwallon Kwando shine kadai abinda take da burinsa. An haifeta kuma ta girma a kauyen Jingfeng na yankin tsaunin Taiyue, Yao ta rayu cikin yanayin talauci. Kauyawa kimanin 2,000 a Jingfeng basu da ikon samun damar yin daben siminti har zuwa shekara ta 2000. Iyalan Yao sun fada cikin yanayin halin tsananin talauci ne a shekarar 2013, a lokacin da mahaifin Yao Zhansheng ya kamu da cutar mafitsara kana yana bukatar a yi masa dashen koda. Mahaifiyarta Duan Jian'e, tana son bayar da gudunmowar kodarta daya domin ceto mijinta, amma wadan nan iyalai basu da sukunin biyan kudin aikin tiyatar dashen kodar. Bisa taimakon gwamnatin karamar hukumar da kuma rancen kudi daga wasu 'yan uwa da makwabta, an ceto rayuwar mahaifin Yao, sai dai an umarceshi ya cigaba da shan magani na tsawon lokaci lamarin da ya sanyashi barin aikinsa. Al'amurra sun canza a shekarar 2017 a lokacin da aka samar da wata dama wajen raya cigaban fannin yawon shakatawa a yankunan karkara dake wannan kauyen karkashin wani shigin gwamnati na kokarin yaki da fatara. Iyalan Yao sun fara farfadowa sannu a hankali, kana sun yi nasarar fita daga kangin fatara a shekarar 2018. A wannan lokaci ne Yao ta fara wasan kwallon Kwando, kuma ta nuna bajintarta game da wasan. Duk da rashin samun damammaki, wasan kwallon Kwando na tsaunin Taiyue yayi matukar shahara a wannan yanki. A yankin Qinyuan, inda a can ne kauyen Yao yake, kuma duk da kasancewar yawan alummar kauyen 160,000, akwai kungiyoyin wasan kwallon kwando 306 da filayen wasanni 218. Sha'awar wasan yana cigaba da kara ratsa zuciyar Yao a koda yaushe. An gina filin wasan kwallon Kwando a makarantar firamaren kauyen su Yao a shekarar 2017. Kuma a lokacin da Yao ta fara buga wasan kwallon Kwando a karon farko kungiyoyin wasanni biyu kawai aka kafa wadanda ke kunshe da daliba 'yan wasa 37 kacal. A bara, Yao Ming da kungiyar wasan kwallon Kwando ta kasar Sin sun fara aikin shiryawa kananan yara wasannin kwallon Kwando 'yan tsakanin shekaru 6 zuwa 12. Shugaban kungiyar kwallon Kwando ta kasar Sin CBA, na son bunkasa karamar kungiyar kwallon Kwandon, shirin ya kunshi samar da karamar ragar wasa, da karamar kwallo, da kuma karamin filin wasan kwallon kwandon. Liu Yalin, shugaban babbar makarantar firamary ta Jingfeng yace, dole su shiga a dama dasu a harkokin wasannin karamar kwallon kwando. Yan wasan kwallon Kwando na firamaren suna sha'awar shiga ainihin gasar kwallon Kwando wacce ake gudanarwa a yankin. Don haka Liu ya fara tuanin zabar wadanda zasu wakilci makarantar da kuma kungiyar Yao, dukkan yara mata, sun nunawa yara maza cewa zasu iya samun gurbi a wasannin da ake shiryawa a yankin. To sai dai kuma, an bukaci shugaban makarantar Liu, da ya aika da sunayen 'yan kungiyar wasa yara maza domin su wakilci Jingfeng, saboda babu wasu daga cikin abokan karawarsu da suka aike da tawagar 'yan wasa mata. Sai wani muhimmin tunani ya fadowa Liu. Sai ya kafa wata kungiyar 'yan wasa ta hadin gambiza wacce ta kunshi yara maza da mata, kuma sai aka zabi Yao. Kungiyar wasan ta hadin gambizar ta samu matsayi na 4 a gasar wasannin yankin. A lokacin gasar, hazakar da Yao ta nuna ya burge dukkannin masu kallon wasan hakan yasa aka baiwa kungiyar suna na U12 squad ta birnin Changzhi a shekarar 2018. A gasar matakin lardi, kungiyar Changzhi ta yi nasarar shiga jerin kungiyoyi hudu dake sahun gaba. Bisa la'akari da irin rawar da Yao ta taka a wasannin, Wang Gaihuan, babban mai horas da 'yan wasa na kungiyar wasan makarantar Jinshan Middle School, ya yanke shawarar daukar yarinyar aiki. Wang ya fada a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Xinhua cewa, "yanayin shigar da tayi na kayan wasa riga da kalmi, da irin juriyar da take dashi, al'amarin yayi matukar bugeni sama da yadda wasu 'yan wasan ke yi a lokacin buga wasan kwallon Kwando". Wang yace, "A lokacin da na tambayeta ko tana sha'awar zuwa buga wasan kwallon kwando, Yao tace eh. A wancan lokacin, naga alamun himma da kwazo a fuskarta. Daga nan sai na fadawa kaina cewa zan yi iyakar kokarina wajen koyar da ita." Yao bata bashi kunya ba. Tana kokarin samun cikakken horo a kullum bayan an tashi daga makaranta. Bayan data haye matsalar kangin talauci da sauran wahalhalun rayuwa, a yanzu tana da burin da take son cimma na samun galaba akan dukkan abokan karawarta a filin wasan.

"Ina so wata rana na kai matsayin da zan fafata a matakin wasa na kasa, kuma idan wannan lokacin ya tabbata ina son zuwa Beijing tare da iyalaina," inji Yao.(Ahmad Fagam)