logo

HAUSA

Ramos Ya Kafa Sabon Tarihi A Real Madrid

2019-08-28 08:44:36 CRI

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos, wanda kuma shi ne kyaftin din kungiyar sannan kuma kaftin din tawagar 'yan wasan kasar Sipaniya ya kafa sabon tarihi a kungiyar a satin da ya gabata. Real Madrid ta fara gasar La Liga ta bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke kungiyar kwallon kafa ta Celta Vigo daci 3-1 a wasan makon farko ranar Asabar din da ta gabata duk da cewa an ba wa Dan wasa Luca Modric jan kati Sergio Ramos ya buga wasan da Real ta yi a filin wasa na Balaidos, wanda shi ne na 283 da Madrid ta yi nasara a La Liga tare da kyaftin din nata kuma hakan ne ya sa ya yi kan-kan-kan da tsohon dan wasan kungiyar, Gento, a mataki na hudu a jerin 'yan Real Madrid da ta ci wasannin La Liga da dama a cikin fili. Real ta ci kwallayen ta hanun Karim Benzema da Toni Kroos da kuma Lucas Bazkuez, yayin da Celta ta zare daya daf da za a tashi daga wasan ta hannun Iker Losada duk da cewa takai muna nan hare-hare a wasan. Ramos ya yi wasanni 420 aka ci wasanni 283 da shi a La Liga, shi kuwa Gento ya yi wa Real Madrid fafatawa 427 aka ci wasa iri daya da na Ramos da shi a fili sai dai babu lissafin wasannin da sukayi rashin nasara suna cikin fili. Wadan da ke kan gaba a yawan nasara a Real Madrid a La Liga sun hada da Sanchís wanda aka ci wasanni 312 da shi a mataki na uku sai Raúl mai nasarar wasanni 327 na biyu da Casillas da aka ci wasannin La Liga 334 yana tsaron raga. Wannan ce kaka ta 15 da Ramos ke buga gasar La Liga a Real Madrid, kuma shi ne na bakwai a jerin 'yan wasan da suka buga wa kungiyar wasanni da yawa sannan kuma kyaftin din ya ci kwallo 59 a gasar ta La Liga a shekara 15 da yake buga wasannin, kuma a kakar wasa ta 2016 zuwa 2017 ce ya fi zura kwallaye a gasar, wanda ya ci 7. Ranar Juma'a 23 ga watan Agusta za a fara wasannin mako na biyu a La Liga, inda Real Madrid za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Real Balladolid a filin wasa na Santiago Bernabeu ranar Asabar.