logo

HAUSA

Burin yaran kasar Kenya na taka leda

2019-08-28 08:47:54 CRI

Ana iya ganin yara da dama masu sha'awa da burin zama taurari a fannin kwallon kafa a sassan kasashen duniya. A kasar Kenya wani kwararre, kuma tsohon dan wasan kwallon kafa Godfrey masolo, ya bude makaranta domin horas da matasa masu sha'awar koyon taka leda. Sama da rabin yaran dake wannan cibiyar horo yara ne na unguwannin marasa galihu, da marayu. Suna sha'awar kwallon kafa da kuma burin amfani da wasan wajen sauya rayuwar su. Abokin aiki Yang qiong ya hada mana rahoto daga Kenya. Godfrey masolo, kocin kwallon kafa ne mai shekaru 45 da haihuwa. Shi ne kuma ke gudanar da makarantar kwallon kafa mai lakabin "365 football". A baya Masolo ya taba buga kwallon kafa a wata kungiyar ajin kusa da na kwararru dake Jamus. Bayan barin kwallon kafa sakamakon rauni da ya ji a kafa, sai ya koma Kenya ya fara aiki da wani ofishin MDD dake birnin Nairobi tsawon shekaru 8. Sai dai duk da hakan, ya ci gaba da kasancewa mai mafarkin raya wasan kwallon kafa, burin sa shi ne baiwa karin yaran kasar Kenya damar cika burin su na kwallon kafa. "A yau mun hadu ne domin koyar da kwallon kafa ga yara 'yan tsakanin shekaru 5 zuwa 18, mafi yawan su daga kikuyus da kewaye. Ina fatan ganin sun zo sun buga kwallo, su kaucewa shiga aikata laifuka, da karya doka, da ta'ammali da miyagun kwayoyi da dai sauran su. Sama da rabin dalibai 60 ko 70 na makarantar masolo yara ne daga iyalai marasa galihu da kuma marayu. Suna koyon kwallon kafa kyauta a nan. Domin samar da kudade, masolo kan shirya asusun samar da tallafi a wurare irin su manyan shagunan sayar da kayayyaki –Yana fatan sauya rayuwar wadannan yara ta hanyar kwallon kafa.   "Fata na shi ne fadawa yaran cewa suna da matukar basira, kuma kwallon kafa wata dama ce a gare su, cewa idan sun yi aiki tukuru, suna iya yin rayuwa mai nagarta, su gina idajen su, har ma su taimakawa wasu yaran." Damaris, yarinya ce mai shekaru 19 da haihuwa, ta zo ne daga gidan marayu. Ta fara buga kwallon kafa tun lokacin da ta kammala makarantar sakandare. Ta bayyanawa manema labarai cewa, gwanin ta shi ne messi, tana kuma fatan wata rana za ta kai ga bugawa kasar ta kwallo, kamar yadda shi ma messi ke bugawa kasar sa. "Ina son samun ci gaba har na kai ga bugawa kasar Kenya kwallo a matsayi na na mace." Trevor, yaro ne mai shekaru 12 a duniya, ya kuma fara buga kwallo tun yana kusan shekaru 5. Yanzu yana filin kwallo, suna buga wasa, yana da kwarewa sosai. Sakamakon tasirin mahaifin sa, ya samu sha'awar kwallo da manyan 'yan kwallo irin su ronaldo. Burin sa shi ma shi ne zama wani tauraron dan wasa. "Ina da burin zama tauraron dan wasan kwallo. A matsayi na na cikakken dan wasan motsa jiki, zan zan iya zama tauraro, na kuma samu kudu." Kamar dai a sauran wurare na duniya, ga masu sha'awar kwallon kafa, yaran kasar Kenya ba a filaye manyan kadai suke taka leda ba: su kan yi wasa a tituna, da bakin ruwa, da kan ciyayi. Masolo ya ce wasu daga yaran da yake horaswa su 365, sun fara buga kwallo a kulaflikan kasashen waje.

"Tuni mun fara samun 'yan wasa dake kwallo a Sundan ta kudu da Koriya ta kudu. Na sanya wani a shafin sada zumunta, kuma wani kulaf na Koriya ta kudu ya dauke shi wasa."