logo

HAUSA

Aminatu Adamu

2019-08-20 16:23:42 CRI

Yau shirin In ba ku ba gida na farin cikin gabatar muku wata bakuwa daga Bauchi, tarayyar Najeriya, wato Aminatu Adamu, wadda ke karatun ilmin kimiyya a birnin Jinzhou da ke arewa maso gabashin kasar Sin.

A cikin zantawar da wakiliyarmu Fa'iza Mustapha ta yi da ita, Aminatu Adamu ta yi bayani kan yadda take karatu da zama a nan kasar Sin, da ma yadda ci gaban kasar Sin ya burge ta sosai. Bugu da kari kuma, a matsayinta ta mace, a cikin wannan shirin namu na "In ba ku ba gida", Hajiya ta yi tsokaci kan muhimmancin samun ilmi, musamman ma ga mata. A ganinta ilmi jigo ne na rayuwa, don haka Aminatu ta yi kira ga mata da su tashi su samu ilmi kada su nemi dogaro kan saura.