logo

HAUSA

Li Na, ta zama tauraruwar tennis bayan da fari ta yi adawa da wasan

2019-08-08 16:48:55 CRI

Li Na, daya ce daga mafiya shahara a 'yan wasa da kasar Sin ta taba yayewa, ta kuma zamo tauraruwa da ta yi matukar haskawa a fagen kwallon tennis a mataki na kasa da kasa. Cikin manyan nasarori da ta cimma a wannan fage, akwai lashe kofin "Grand Slam" ta daidaikun yan wasa har karo biyu, kana ta shiga jerin 'yan wasa mafiya shahara a fagen tenis ko "International Tennis Hall of Fame" a turance, matsayin da ta samu a ranar Asabar a karshen mako" bayan jefa kuri'un amincewa da hakan da aka gudanar a tsibirin Rhode Island na Amurka. Da wannan matsayi dai Li ta zama 'yar nahiyar Asiya ta farko da ta samu irin wannan daukaka. Shekarar bana ce dai ta farko, da aka yi amfani da kuri'un masu sha'awar wasan tenis, domin zabo 'yan wasan da za su shiga wannan mataki na daukaka. An kada kuri'u tsakanin kasashe da yankuna 130 dake sassan duniya, kuma sakamakon ya baiwa Li nasarar kasanewa ta daya cikin ragowar 'yan wasa 8 da suka shiga takara. Da take tsokaci game da hakan, Li mai shekaru 37 da haihuwa ta ce, wannan matsayi da ta samu ya cika mata burin ta na rayuwa. Ta ce "na fara wasan tennis tun ina da shekaru 8 a duniya. A lokacin bana son wasan tennis, saboda yana hana ni damar wasa da kawaye na a makaranta." Amma bayan wani dan lokaci, na fara matukar sha'awar wasan. Tennis ya yawata da ni sassan duniya da dama, ya bani damar kewaya kasashe mabanbanta. Ta ce "A nan gaba, zan yi iyakacin kokari na domin karfafa gwiwar karin 'yan wasa matasa, domin su cimma burin su na zama taurari a fagen wannan wasa mai ban sha'awa." Li ta kan bayyana alakar ta da wasan tennis da cewa "kaunace da kiyayya". Ta ce lokacin tana karama, ta sha fama wajen horo da atisaye, masu horaswa na da matsi sosai. Kuma bayan da ta tasa, ta rika sanya 'yan kunne da zanen jiki na tattoo- wanda ba kasafai ake ganin 'yan wasan kasar Sin da wannan dabi'a ba. Kaza lika ta taba bayyana rashin gamsuwar ta a fili, game da yanayin koyar da wasan Tennis na kasar Sin, wanda kuma shi ne ya samar mata da kwarewa. Duk dai da wadannan kalubale da ta fuskanta a lokutan da take kara kwarewa, Li ta kai ga matsayin daukaka, inda ta lashe manyan gasannin Tennis 9, wadanda ake bugawa a kan ciyawa, da na tabo da na tsandauri, aka kuma sanya ta matsayi na 2 a duniya a shekarar 2014. 'Yar wasa ce da ta karya shingaye wajen cimma manyan nasarori a tarihi, inda ta zamo mace ta farko da ta kai ga lashe babbar gasar "Grand Slam" ta daidaikun 'yan wasa daga kasar Sin da ma nahiyar Asiya baki daya, a gasar French Open ta shekarar 2011, matsayin da ta sake samu a shekarar 2014, bayan lashe gasar Australian Open ta shekarar. Wani abun lura a nan shi ne, Li 'yar wasa ce da aka haifa cikin iyali da ke sha'awar wasanni. Ta yi matukar shakuwa da mahaifin ta, wanda ke buga wasan kwallon badminton, ya kuma yi fatan ita ma ta koyi wasan. Sai dai bayan shekaru 2 tana samun horo, kocin Li ya shaidawa mahaifin ta cewa, kwallon tennis ce ta fi dacewa da 'yar sa. Tun lokacin da mahaifin na ta ya ga Li ta rike racket na buga kwallon tennis, ya yi matukar farin ciki, ya san cewa 'yar sa za ta kai wani matsayin bajimta a wannan wasa. Ai kuwa Li ba ta kunyata mahaifin ta ba, domin kuwa ta rika samun ci gaba sannu a hankali. Sai dai rashin lafiyar zuciya ta ritsa da mahaifin ta lokacin da take shekaru 14 da haihuwa, wanda hakan yayi ajalinsa. Daga lokacin ne kuma Li ta lura cewa, kwallon tennis ce damar ta ta daukar dawainiyar iyalin ta. Don haka ta matsa kaimi wajen samun horo domin cika burin mahaifin ta na buga babbar gasar kasar Sin, inda daga karshe ta kai ga hakan, har ma ta lashe lambar zinari a gasar. A gasar kasar Sin ta shekarar 2001, Li ta lashe lambobin zinari 3, ta hau mimbarin karbar kyautukan bajimta da mahaifin ta bai taba kaiwa ba. Amma kuma bayan lashe wadannan lambobin yabo na kasa, ta gamu da wasu matsaloli na rashin lafiya da zabin kashin kai. Daga lokacin ne kuma ita da Jiang Shan, wanda suke buga wasa tare, wanda kuma daga baya ya aure ta suka koma karatu a kwaleji, inda rayuwa ta sauya aka ajiye tennis gefe guda. Li ta ce shekaru 2 da ta yi a jami'a sun ba ta damar yin nazari game da rayuwar ta, da kuma kwallon tennis, da ma irin buri da ta samu na sake komawa fagen wasan. Daga karshe dai ta yanke shawarar komawa wasan ba tare da aniyar sake dakatawa ba. A shekarar 2011, lokacin da ta buga wasa a gasar French Open, a Roland Garros, al'ummar Sin kimanin miliyan 116 sun kalli wasan ta na karshe ta kafar talabijin. A shekarar 2013, Chris Evert dan wasan tennis da ya lashe gasar Grand Slam har sau 18 ya bayyana cewa "Sin ta samu ci gaba a fagen wasan tennis, inda 'yan kasar kusan miliyan 15 ke buga wasan, kuma idan ba domin gudummawar Li ba, da hakan bata faru ba. Li ta zamo 'yar wasa mafi tasiri a kasar Sin. Kafin nasarar lashe French Open a shekarar 2011, ana buga gasannin tenis ajin kwararru 2 ne a kasar Sin. Amma a shekarar nan ta 2019, ana buga irin wadannan gasanni har 11. Yanzu Sin na da 'yan wasan tennis 10 dake cikin sahun manyan 'yan wasan duniya mafiya kwarewa 200, masu buga gasar daidaikun 'yan wasa, da kuma 'yan wasa 13 dake jerin 'yan wasa mafiya kwarewa 200, masu buga gasar 'yan wasa biyu biyu. Yayin da kuma sabbin 'yan wasa ke karuwa a matakin farko. Li ta shahara a fannin ban dariya, da kuma fushi mai tsanani. Ita da kan ta ta taba cewa "Ina da fushi kamar tartsatsin wuta, idan na fusata ina matukar hasala". Ga wadanda suka san ta, wannan ba wani abu ne mai ban mamaki ba, duba da cewa, an sha ganin ta tana yiwa mijin ta tsawa a lokutan da suke buga wasa tare. A shekarar 2011 yayin wasan karshe na Australian Open, Li ta bayyana cewa: "Ina matukar zolayar miji na, amma ba wani abun damuwa kasancewar sa siriri ko lukuti, kyakkyawa ko mummuna, har abada zan bi ka, kuma ina kaunar ka." Kaza lika a shekarar 2014 yayin wasan karshe na gasar Australian Open, Li ta bayyana cewa: "Max, wakili na, ya sa na yi arziki." Sannan ta juya ta kalli mijin ta, ta ce kai mutum ne na gari. Kuma, ka yi sa'a da ka same ni!. Tun a shekarar 2014 ne dai Li ta bayyana aniyar ta ta dakatar da buga wasan tennis, sai dai kuma shigar da sunan ta cikin jerin 'yan wasa mafiya shahara na "Hall of Fame", ya sake bayyana irin tasirin ta a fagen wasan tennis tsakanin 'yan wasan na Sin, da ma sauran masu buga wasanni daban daban.

Kamar dai yadda Serena Williams ta taba fada, "Li Na, tauraruwa ce a sama, wadda har kullum ke haskawa, kuma har abada ba za ta daina haskawa ba." (Saminu)