Kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da tsaron kasarta
2019-08-07 08:44:21 CRI
A ranar Laraba 24 ga watan Yulin shekarar 2019 ne, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayanai game da manufarta ta tsaron kasa a sabon zamanin da muke ciki kana da yin bayani game da hakikanin matakanta, da manufofin shirin, da kuma muhimmancin kokarin da kasar ke yi na kafa ingantaccen tsarin tsaron kasa da rundunar soji mai karfi.
Babban abin da takardar bayanan ta kunsa sun kasu kashi shida: yanayin tsaron kasa da kasa, manufar tsaron kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki, sauke nauyin dake wuyan dakarun tsaron kasar Sin a sabon zamani, gyare-gyare a fannin tsaron kasar Sin da harkokinta na soji, kasafin kudaden da suka cancanci fannin tsaro, da kuma gudummowar da za'a bayar wajen gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.
Takardar bayanin ta kuma ce kasar Sin na nacewa manufar kare kai karkashin kudurorin ta na tsaron kasa a sabon zamani da ake ciki da bin salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman ta Sin, matakin da ke kunshe da dabarun samar da ci gaba cikin lumana, da manufofin cudanyar kasa da kasa masu zaman kan su, da al'adun gargajiya mafi nagarta dake la'akari da zaman lafiya da lumana a matsayin jigo.
Kaza lika takardar ta jaddada kudurin kasar Sin, na aiwatar da manufofin tsaro a sabon zamani, dake da nufin kare 'yancin mulkin kai, da tsaro da ci gaban al'umma. Kaza lika Sin ba ta da burin yin babakere, ko fadada tasirin ta a wasu sassa ba, wanda hakan shi ma jigo ne na manufofin kasar game da ayyukan soji a sabon zamani da ake ciki.
Daga karshe takardar bayanin ta ce, burin Sin a fannin tsaron kasa shi ne, ci gaba da karfafa tsarin aikin sojoji bisa salon kasar, da mayar da rundunar mai kyakkyawan tasiri a matakin kasa da kasa, fannin gina al'ummu masu makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)