logo

HAUSA

An kwace hodar Cocaine sama da ton 2.2 a Cape Verde

2019-08-06 14:05:18 cri

Jiya Litinin, hukumar 'yan sandan kasar Cape Verde, ta fitar da sanarwar cewa, kwanan baya rundunar 'yan sandan kasar ta kwace hodar Cocaine mai nauyin kilogram 2256, daga wani jirgin ruwa mai daukar kayayyaki a Praia, fadar mulkin kasar.

Sanarwar ta ce, a ranar 3 ga wata, 'yan sandan kasar sun gano hodar Cocaine din mai tarin yawa, a wani jirgin ruwan da ya taso daga kudancin Amurka, sun kuma kama mutane biyar 'yan asalin Brazil. Amma, bangaren 'yan sanda bai fayyace asalin jirgin ruwan ba.

A ranar 31 ga watan Janairun bana ma, 'yan sandan kasar Cape Verde din sun kwashe Cocaine mai nauyin ton 9.5, daga wani jirgin ruwan dakon kaya mau dauke da tutar kasar Panama dake sauke kaya a tashar Praia, aka kuma kama ma'aikatan sa 'yan asalin kasar Rasha su 11. (Bilkisu)