logo

HAUSA

Kenya ta samu tsallake zagayen farko na kasashe dake neman gurbin buga gasar cin kofin duniya na 2022

2019-08-01 08:38:31 CRI

Kungiyar kwallon kafar kasar Kenya, ta shiga jerin kasashen Afirka 26 da aka baiwa damar kai tsaye, ta wuce zagayen farko na buga wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya da hukumar FIFA ke shiryawa, gasar da za ta gudana a shekarar 2022 a kasar Qatar. Hukumar kwallon kafar kasashen Afirka ko CAF a takaice, ta ce kungiyoyin kasashe 14 da suka wuce zagayen neman gurbin na farko, da kasashe 26 da aka yafewa buga wannan zagaye, za a raba su rukunoni 10 sau 4, wato za su zamo kungiyoyi 40 ke nan. Za a fara buga wasannin zagaye na farko a cikin watan Satumba dake tafe, a kuma buga zagaye na biyu a watan Maris na shekarar 2020. Kungiyoyin da aka baiwa damar tsallake zagayen wasannin neman gurbin na farko dai sun hada da Senegal, da Tunisia, da Najeriya, da Algeria, da Morocco, da Masar, da Ghana, da Kamaru. Sai kuma janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Cote d'Ivoire, da Mali, da Burkina Faso, da Afirka ta kudu, da Guinea, da Cape Verde, da Uganda. Akwai kuma Zambia, da Benin, da Gabon, Congo, da Madagascar, da Nijar, da Libya, da Mauritania, da Kenya, da janhuriyar tsakiyar Afirka.

A tsarin wasannin da za a buga, an hada kasashe masu rauni 28, ciki hadda Burundi da za ta taka wasa da Tanzania, kasashe biyu daga gabashin Afirka, wadanda kuma suka taka leda a gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON, wanda aka kammala ba da jimawa ba.(Saminu)