Ranar yawan al'umma ta duniya ta shekarar 2019
2019-08-01 09:17:46 CRI
Ana bikin wannan rana ce a ranar 11 ga watan Yulin kowa ce shekara. Kuma majalisar gudanarwar shirin raya kasashe na MDD(UNDP) ne ta bullo da wannan rana a shekarar 1989, don mayar da hankali kan bukatar gaggauwa mai muhimmanci kan batutuwan da suka shafi yawan al'umma a duniya.
A bana, ranar ta bukaci kasashen duniya, da su mayar da hankali kan batutuwan da ba a kai ga kammalawa ba a taron shekarar 1994 game da yawan al'ummar duniya da ci gaba, inda gwamnatocin kasashe 179 suka amince cewa, batun lafiyar mata masu juna da daidaiton jinsi, suna da muhimmanci ga batun samun ci gaba mai dorewa.
Ana kuma amfani da wannan rana, wajen Ilimantar da jama'a game da batutuwan da suka shafi yawan al'umma, kamar muhimmancin tsara iyali da daidaiton jinsi da matsalar talauci da lafiyar mata da kuma 'yancin bil-Adam. Bayanai na nuna cewa, a irin wannan rana, a kan shirya gasar rubutun zube,da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, ana kuma lika kyallaye da takardu da aka rubuta sakonni da hotunan ilimantar da jama'a game da bunkasar al'umma da yadda hakan ka iya haifar da illa ko wata matsala ga rayuwar jama'a.
Wani sabon rahoto da MDD ta fitar, ya nuna cwa, yanzu haka yawan al'ummar duniya ya kai biliyan 7.7. kuma nan da shekaru 30 masu zuwa wato shekarar 2050, za a samu karuwar mutane biliyan biyu(2) daga biliyan 7.7 zuwa biliyan 9.7.
Masana na cewa, wajibi ne gwamnatoci da kungiyoyin fararen hula gami da na kasa da kasa da daidaikun jama'a, su dauki matakan da suka dace don warware matsalar da yawan al'umma ka iya haifarwa ga rayuwar bil-Adam da ma duniyar baki daya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)