logo

HAUSA

Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Madrid Ta Hana Bale Tafiya Kasar China?

2019-08-01 08:35:57 CRI

Published 3 hours ago on July 30, 2019 By Abba Ibrahim Wada Real Madrid ta hana shirin da dan wasanta Gareth Bale ke yi na koma wa kungiyar kwallon kafa ta Jiangsu Suning ta kasar Sin, wato China, domin cigaba da buga wasa, wanda hakan ya sa yanzu babu maganar tafiyarsa zuwa yankin na Gabas Mai Nisa. Tun farko an sa ran Bale, dan kwallon tawagar Wales, zai koma buga gasar China kan yarjejeniyar shekara uku kan fam miliyan daya da zai dunga karba kowanne mako idan har ya amince. A can baya kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane ya fayyace cewar Bale ba ya cikin tsarinsa, kuma ya na fama da jinyar rauni, domin wasan La Liga 79 ya buga a kaka wasanni hudu da ya yi a kungiyar. A makon jiya Zidane ya ce Bale ya kusan barin Real, kuma hakan zai amfani dan wasan da kungiyar da zai koma da ita Madrid din gabannin karawar sada zumunta da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich. Hakan ne ya sa Real ya maida hankali kan kudin da za ta sayar da Bale ga duk kungiyar da ta ke bukatar daukar shi a bana sai dai sakamakon dokar da hukumar kula da kwallon kafar kasar China ta sa ya sa dole a hakura da cinikin. Kamar yadda dokar ta ke, dole kowacce kungiya wadda ta ke buga gasar rukuni-rukuni ta kasar kada ta dauki 'yan wasa guda biyar wadanda ba 'yan kasar China ba. Hakan yana nufin yanzu 'yan wasan da su ke cikin kungiyar sun kai biyar wadanda ba 'yan kasar ba kuma Bale ba zai samu shiga ba. Bale ya koma Real Madrid a shekara ta 2013 kan fam miliyan 85, a matsayin mafi tsada a duniya, ya kuma taimakawa kungiyar ta lashe kofin Zakarun Turai hudu a zamansa a kungiyar sai dai dan wasan tawagar Wales din ya buga wa Real Madrid wasanni biyu na atisayen tunkarar kaka mai zuwa, inda ya ci kwallo a wasan da suka yi 2-2 da Arsenal. Haka kuma ya buga minti 30 a karawar da Atletico Madrid ta doke Real Madrid 7-3 a wasan hamayya a dai atisayen tunkarar kakar bana kuma wakilin Bale a harkokin kwallon kafa, Jonathan Barnet ya bayyana Zidane a matsayin mara kirki kan yadda ya dauki batun Bale, ya kuma ce duk cinikin da za su yi sai dai ya amfani wanda yake wakilta.(Amina Xu)