logo

HAUSA

Iker Casillas ya karbi mukamin kociyan Porto

2019-08-01 08:37:44 CRI

Tsohon mai tsaron ragar Spain Iker Casillas ya samu zama kociyan kungiyar wasan FC Porto wanda yake yiwa aiki a halin yanzu a yayin da yake kara murmurewa daga cutar bugun zuciya dake damunsa wanda ya kamu da jinyar a lokacin fara shirin horas da 'yan wasa a watan Mayu. Matakin ya zo ne bayan da Casillas ya koma samun horo a kungiyar wasan Portugal a ranar 1 ga watan Yuli, watanni biyu bayan da ya kamu da cutar bugun zuciyar. A wata sanarwar da aka wallafa a shafin intanet na kungiyar Porto, ta bayyana dan wasan mai shekaru 38 wanda yayi nasara a gasar kofin duniya na 2010, zai tabbatar da an samu kyakkyawar alaka tsakanin 'yan wasa, da kociya, da hukumar gudanarwar kungiyar wasan. "Zan yi iyakar bakin kokarina wajen taimakawa 'yan wasan kungiyata," inji Casillas, ya kara da cewa "manaja [Sergio Conceicao] yayi magana da ni a kakar wasannin data gabata a lokacin al'amarin ya faru dani kuma ya fada mini cewa yana son na cigaba da zama tare dasu, domin kusanci da 'yan wasan, zama kusa da matasan 'yan wasan, saboda za'a samu sauye sauye masu yawa."

Casillas ya ki cigaba da aikin wasanni a wasu kwanaki ne, sakamakon bugun zuciyar da ya sameshi, kuma dawowar da yayi wajen horas da 'yan wasan alamu ne dake nuna cewa zai cigaba da aiki wanda ya sha fitowa har sau 725 a kungiyar wasan Real Madrid, sau 156 a Porto, kana ya taka leda sau 167 ga Spain, amma a yanzu kamar alamu na nuna cewa zai iya yin murabus daga wasa bayan shafe shekaru 20 a fagen wasanni.