Namibia ta zabi kociyan da zai horas da yan wasan kasar a gasar kofin kwararru na Afrika a 2020
2019-08-01 08:36:53 CRI
Kwamitin tsare tsare na hukumar FIFA ya sanar cewa an zabi Bobby Samaria, a matsayin mutumin da zai jagoranci horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Namibia a gasar kofin kwararru ta kasashen Afrika (CHAN) tsakanin 26 ga watan Yuli zuwa 2 ga watan Augastan shekarar 2020. Shugaban kwamitin tsare tsare na FIFA Hilda Basson-Namundjebo, ya tabbatar da cewa, Samaria ya sake dawowa babbar kungiyar wasan ne bayan da ya barta na wasu lokuta a baya. Yace sun samu kociyan da zai horas da tawagar 'yan wasan a gasar CHAN, kuma sun yi amanna cewa Bobby yana da cikakkiyar kwarewa da zai iya jagorantar horas da 'yan wasan da kuma gina ingantaccen tsari ga kungiyar wasan. Kuma ba zasu taba yin sakaci da wannan muhimmiyar damar da suka samu ba a wasan share fagen kuma tuni har tawagar 'yan wasan sun fara samun horo a ranar Talata. Samaria, wanda ya taba samun nasarar lashe kyautar Namibian league na kwararrun Afrika a shekarun 2009, 2010 da 2017, ya zabo 'yan wasan 31 don hada kungiyar wasan domin basu horo.
Samaria yace a ranar 22 ga watan Yuli ne tawagar ta shirya isa Comoros kuma yana cigaba da nanata aniyarsa na tabbatar da shirin horas da 'yan wasan.(Ahmad, Amina Xu)