Taron karawa juna sani game da hadin-gwiwar raya ilimi da al'adu tsakanin Sin da Afirka
2019-07-30 14:22:34 CRI
A kwanakin baya ne aka yi taron karawa juna sani na kasa da kasa game da hadin-gwiwar raya ilimi da al'adu tsakanin Sin da Afirka a jami'ar horas da malamai ta lardin Zhejiang ko kuma Zhejiang Normal University a turance a birnin Jinhua na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. A yayin taron, an kuma kaddamar da cibiyar bincike game da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin raya ilimi. Kana an gabatar da rahoton shekara game da musaya tsakanin masanan Sin da na Afirka ta Kudu. Har ila yau, an sanya hannu kan takardar fahimtar juna ta kulla hadin gwiwa tsakanin jami'ar horas da malamai ta lardin Zhejiang da jami'ar Modibbo Adama ta Yolar jihar Adamawa, da kuma jami'ar Ibadan dukka daga tarayyar Najeriya. Masana da jagororin wasu hukumomin Sin da na jami'o'in Najeriya ne suka halarci wannan taro. Daga Najeriya kuwa, taron ya samu halartar mataimakin shugaban jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya dake Jos farfesa Seddi Sebastian Maimako, da mataimakin shugaban jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Ibadan farfesa Adebola Babatunde Ekanola, da takwaransa na jami'ar Modibbo Adama dake birnin Yolar jihar Adamawa farfesa Usman Abdullahi Wurochekke, da kuma mukaddashin mataimakin shugaban jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya dake Benin Micheal Emefiele Aziken da dai sauransu. Mahalartan sun gabatar da makaloli da dama, wadanda suka kunshi irin kalubale dake tattare da burin da ake da shi, na inganta samar da ilimi a manyan makarantun Najeriya, da irin rawar da hadin gwiwar jami'o'in Sin da na Najeriya zai taka, wajen cimma moriyar juna tsakanin sassan biyu.
A yayin wannan taro, wakilinmu Saminu Alhassan ya samu zantawa da mataimakin shugaban jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Modibbo Adama dake birnin Yolar jihar Adamawa, wato farfesa Usman Abdullahi Wurochekke, game da dalilin da ya sanya jami'arsa ta ga dacewar kulla alaka da jami'ar horas da malamai ta Zhejiang dake birnin Jinhua, kuma shaihun malamin ya amsa wannan tambaya, tare da yin karin haske game da tasirin ilimi ga rayuwar bil'adama.(Murtala Zhang)