Ya kamata FINA ta dauki matakan kin amincewa da ayyukan nuna rashin girmamawa ga Sun Yang
2019-07-26 08:40:23 CRI
A gun bikin bada lambobin yabo na wasan ninkaya cikin 'yanci na zango mita 200 na gasar wasan iyo ta kasa da kasa da aka gudanar a daren ranar 23 ga wata, da gangan dan wasan kasar Birtaniya Duncan Scott ya ki musafaha, da daukar hoto tare da dan wasan kasar Sin Sun Yang. Wannan ne karo na biyu da wani 'dan wasan kasashen waje ya yi hakan a gun gasar ta wannan karo. Wannan ba shi ne karo na farko da lamarin kin daukar hoto tare da Sun Yang ya faru ba. Kafin hakan, dan wasan Australia Mack Horton ya ki tsayawa tare da Sun Yang, yayin da ake bayar da lambobin yabo gare su, bayan da Horton ya koma kauyen 'yan wasa, kuma wasu 'yan wasan kasashen yammacin duniya sun maida shi a matsayin jarumi, kamar su ne masu tabbatar da odar wasan iyo. Watakila a wasanni masu zuwa, idan Sun Yang ya sake samun lambobin yabo, saidai wasu 'yan wasan za su iya aikata irin wannan halayya. An maida hankali daga wasan iyo zuwa bikin bada lambobin yabo, a gun gasar wasan iyo ta kasa da kasa, wadannan lamura sun kawo illa ga mutuncin wasan iyo. Don haka ya kamata kungiyar wasan iyo ta duniya wato FINA, ta dauki matakai don yanke hukunci ga 'yan wasa da suka nuna rashin ladabi, da nuna rashin girmamawa ga sauran 'yan wasa, ba ma zargin su kadai ba, kamata yayi ma a dakatar da wasansu, ko cin su tara, har ma da soke makinsu a wasan. Amma abun rashin jin dadi shi ne, kungiyar FINA ba ta shaida ikonta na tabbatar da odar wasan iyo ba. Kamar yadda tsohon shugaban gudanarwa na hukumar yaki da shan abubuwa masu kara kuzari ta kasar Australia ya bayyana, dalilin da ya sa wasu 'yan wasa suke nuna kin amincewa da Sun Yang shi ne, domin batun kin yin bincike game da maganin kara kuzari ga Sun Yang a shekarar bara. Amma kungiyar FINA ta riga ta tabbatar da cewa, Sun Yang ba shi da laifi kan batu.
Tawagar Sun Yang ta bayyana cewa, za ta yi hadin gwiwa tare da kungiyar yaki da shan maganin kara kuzari ta duniya, a gun taron sauraron ra'ayoyi a watan Satumba na bana, don shaida wa duniya Sun Yang ba ya shan maganin kara kuzari. (Zainab)