logo

HAUSA

An kaddamar da taron kolin hadin gwiwar zaman lafiya da tsaro na Sin da Afrika a karon farko a Beijing

2019-07-25 09:41:30 CRI

A kwanan baya aka kaddamar da taron kolin dandalin hadin gwiwar zaman lafiya da tsaro na kasashen Sin da Afrika a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin. Taron wanda shine irinsa na farko da aka taba gudanarwa wanda ya samu halartar manyan jami'ai da hafsoshin sojoji na kasashen Sin da Afrika.

Jami'an bangarorin biyu sun gabatar da muhimman jawabai dake shafar yadda bangarorin biyu zasu hada gwiwa da juna wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro musamman a daidai wannan lokaci da ake fama da kalubalolin tsaro da rashin zaman lafiya a sassa daban daban na duniya. Wakilan sojojin kasar Sin da na kasashen Afrika kusan 100 ne suka halarci taron daga kasashen Afrika 50 da wakilan kungiyar tarayyar Afrika AU, an yi kiyasin ministocin tsaro da manyan hafsoshin sojoji na kasashen Afrika 15 ne suka halarci taron kolin na zaman lafiya da tsaro irinsa na farko wanda ma'aikatar tsaron kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa.

A wata sanarwa da Smail Chergui, kwamishinan hukumar zaman lafiya da tsaro na AU ya bayar, ya jadda muhimmancin dandalin wanda a cewarsa zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwar Sin da Afrika ta fannin zaman lafiya da tsaro a kokarin da ake yi na tabbatar da gina ingantaccen zaman lafiya a fadin nahiyar Afrika baki daya. Yace taron kolin ya zo ne a dadai lokacin da Afrika ke kara fuskantar kalubalolin tsaro da zaman lafiya da kuma kokarin da ake na kawo karshen yawan tashe tashen hankula a nahiyar domin samun dawwamamman zaman lafiya a Afrika.

Ya kara da cewa wannan dandali ya kasance a matsayin wata muhimmiyar damace don tattauna muhimman batutuwan zaman lafiya da tsaro karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika, kuma hakan yana kara bayyana irin taimakon da kasar Sin ke bayarwa wajen shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro na nahiyar Afrika. Haka zalika, kwamishinan na AU ya yabawa gwamnatin kasar Sin sakamakon tunanin da tayi na kaddamar da wannan muhimmmin dandali na hadin gwiwar Sin da Afrika kan batun zaman lafiya da tsaro irinsa na farko.

Da yake tsokaci game da irin kokarin da AU ke yi wajen rigakafin afkuwar tashe tashen hankula a nahiyar, Chergui ya ce, kungiyar ta AU mai mambobin kasashe 55, ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile matsalolin rikice rikicen da suka shafi zabuka da sauran tashe tashen hankula wadanda ke haddasa rashin kwanciyar hankali musamman rikice rikice tsakanin gwamnatoci da kungiyoyin 'yan hamayya, nasarorin sun tabbata ne ta hanyar tura jami'an aikin wanzar da zaman lafiya da tsaro. Mista Chergiu ya ce, wannan ne dalilin da yasa suke matukar farin ciki sakamakon kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin kungiyar tarayayyar Afrika AU da gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin bisa goyon bayan shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar ta AU.

A cewar kungiyar ta AU, gwamnatin kasar Sin ta jima tana tallafawa shirin wanzar zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU a Somaliya AMISOM, wato tun a shekarar 2011, ta hanyar samar da tallafin kayayyakin aiki, da kudaden gudanarwa wanda aka kiyasta gwamnatin Sin tana kashe kimanin dalar Amurka miliya 1.2 a duk shekara. Bugu da kari, kasar Sin tana samar da tallafi ga dakarun shirin ko-ta-kwana na wanzar da zaman lafiya na Afrika ta hanyar samar musu da kayayyakin aiki wanda aka kiyasa kudin kan dala miliyan 100.

Da yake jawabi a madadin wakilan kasashen Afrika, Hamed Bakayoko, ministan tsaron kasar Kodebuwa yace, suna fata taron kolin zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwar Sin da Afrika wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, ta yadda bangarorin biyu zasu cimma nasarar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Afrika har ma ga duniya baki daya. (Ahmad Fagam, Ibrahim Yaya/ Sanusi Chen)