logo

HAUSA

Aljeriya ta kai wasan karshe a gasar AFCON bayan doke Najeriya

2019-07-17 10:40:31 CRI

Dan wasan Manchester City Riyad Mahrez ya yi nasarar jefa kwallo a bugun tazara a minti na karshe na wasan kusa da na karshe na gasar AFCON da Aljeriya ta bugu da Najeriya a daren ranar Lahadi, inda ta doke Najeriya da ci biyu da 1. Matakin da ya baiwa Aljeriyar damar kaiwa ga wasan karshe na gasar. Mahrez wanda aka bayyana a matsayin gwarzon dan wasa, ya ce, Najeriya ba kwanwar lasa ba ce. A nasa tsokacin mai horas da 'yan wasan Aljeriya Djamel Belmadi, ya ce, ya san cewa, wasan zai yi zafi, saboda karfin tawagar Najeriyar da ma yadda 'yan wasan na Aljeriya suka gaji. Najeriya ta yi nasarar jefa kwallonta ne a mituna 71 na wasan, a bugun daga kai sai mai tsaron gida ta hannun dan wasan gabanta Odion Ighalo dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua dake kasar Sin, bayan da na'urar dake taimakawa alkalin wasa ta tabbatar da cewa, dan wasan Aljeriya ya taba kwallon da hannu. Mai horas da 'yan wasan Najeriya Gernot Rohr, ya amince cewa, 'yan wasan gaba Aljeriya sun matsawa masu tsaron bayan Najeriya lamba, abin da ya sa suka rude. A ranar 21 ga watan Yuni ne dai aka bude gasar cin kofin kwallon kafan Afirka na 32 a kasar Masar. Za kuma a kammala gasar ce a ranar Jumma'a 19 ga watan na Yulin, inda za a

buga wasan karshe tsakanin Aljeriya wadda ta lashe kofin gasar a shekarar 1990 da kasar Senegal wadda ta doke kasar Tunisa da ci 1 da nema a daya wasan kusa da na karshen da aka buga.

Mun Yi Zaton 'Yan Wasan Algeriya Sun Gaji – Kociyan Najeriya

Mai koyar da tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya, Gernot Rohr, ya bayyana cewa 'yan wasan sa sunyi zaton 'yan wasan kasar Algeriya sun gaji hakan yasa sukayi kokarin ganin sunje karin minti 30 a wasan domin su samu damar samun nasara akansu. Najeriya dai ta samu damar farke kwallon da kasar Algeriya ta cilla mata wanda hakan yasa wasan ya kusa zuwa karin minti 30 sai dai bayan karin minti hudu na wasan dan wasan Manchester City, Riyad Mahrez ya zura kwallo ta biyu a ragar Super Eagles a bugun tazara. Rashin nasarar ne yakawo karshen fatan da Najeriya takeyi na ganin ta lashe gasar a karo na hudu kuma hakan yakawo karshen fatan mai koyarwar na ganin ya lashe babbar gasa da tawagar ta SuperEagles. "Ina ganin wasa ne wanda aka buga shi da kwarewa da nustuwa kuma kowanne bangare ya yi kokarin ganin ya samu nasara sai dai gaba daya 'yan wasa na sunyi zaton Algeriya sun gaji saboda haka sukaso a tafi karin minti 30 domin samun babbar daga akansu" in ji kociyan na Najeriya Ya cigaba da cewa 'Tun da farko da kanmu mukaci gida sai dai daman kamar yadda muka saba a kowanne wasa munyi kokari mun farke ta hanyar bugun fanareti sai dai daga baya kuma ta tabbata cewa sune da nasara saboda haka babu yadda zamuyi da abinda ya zama dole sai ya kasance" A daya wasan kuma kasar Senegal ce tasamu nasarar zuwa wasan karshe bayan ta doke kasar Tunusia daci 1-0 wanda hakan yasa za'a buga wasan neman na uku tsakanin Nigeriya da kasar Tunusia a ranar Laraba a filin wasa na Al-Salam dake babban birnin kasar Masar din wato Cairo.

Zan So Mahrez Ya Sake Buga Min Tazara

Mai tsaron ragar tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles, Daniel Akpeyi, ya kare ragowar 'yan wasan Najeriya da magoya baya suke suka inda yace zaiso ace dan wasa Mahrez ya dawo ya sake bugawa saboda zai iya buge kwallon. Kasar Algeriya dai tayi waje da Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Africa a matakin kusa dana karshe duk da cewa anyi zaton Najeriya ce zata samu nasara a fafatawar ganin kasashen data cire a wasanninta na baya. Sai dai kwallon da dan wasan Manchester City, Riyad Mahrez ya zura a raga a daidai minti na 94 da wasan yasa Najeriya tayi sallama daga gasar ta bana sai dai zata fafata wasan neman na uku da kasar Tunusia. "Abin bakin cikine ace an ciremu daga gasar acikin wannan yanayi kuma magoya baya suna zagin wasu daga cikin 'yan wasa saboda zargin rashin mayar da hankali ko kokari kuma nima zanso ace Mahrez ya dawo domin ya sake bugawa" in ji mai tsaron ragar na Najeriya Ya cigaba da cewa "Duk da haka ba zaka iya hana kowa cewa abinda yake soba sai dai nasan nan gaba muna da 'yan wasan da zasu kawo mana kafin har gida kuma an cire kasashe da dama a gasar sai muyi murna tunda mu har yanzu muna cikin gasar" Najeriya dai zata buga wasan neman na uku da kasar Tunusia kuma sau shida Najeriya tana lashe wasannin neman na uku a tarihin gasar yayinda kuma acikin guda shidan guda hudu daga ciki ba'a iya zura mata kwallo a raga. (Amina Xu, Ibrahim Yaya)