logo

HAUSA

Arsenal Ta Tura Likitoci Domin Gwada Lafiyar Everton Soares

2019-07-17 10:26:30 CRI

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tura wakilanta zuwa kasar Brazil domin gwada lafiyar dan wasa Eberton Soares wanda aka bayyana cewa Arsenal din ta amince zata saya. Arsenal dai ta dade tana zawarcin dan wasan wanda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Gremio dake kasar ta Brazil kuma a gasar cin kofin Coppa America da Brazil ta lashe dan wasan ya zura kwallaye uku a raga. Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana tuni Arsenal ta tura wakilai zuwa birnin Porto Alegre dake kasar Brazil domin gwada lafiyar dan wasan a kokarin da kungiyar takeyi na ganin ta dauki dan wasan tsakiyar wanda zai maye mata gurbin Aaron Ramsey, wanda ya koma Jubentus a kyauta. Tuni dai aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta amince zata biya kungiyar Gremio fam miliyan 25 akan matashin Soares sannan kuma idan dan wasan yayi kokari Arsenal zata karawa Gremio fam miliayn 9 Idan har Arsenal ta dauki dan wasa Soares hakan ya kasance kociyan kungiyar, Unai Emery ya dauki 'yan wasanni biyu kenan bayan da a kwanakin baya kungiyar ta dauki dan wasa Gabriel Martinelli daga kungiyar Ituano. A jiya dai wasu magoya bayan kungiyar suka aike da wata wasika ga shugaban gudanarwar kungiyar, inda suka gargadeshi akan cewa idan har bayason suyiwa kungiyar bore dole sai ya bawa kungiyar kudi wajen sayan 'yan wasa.(Amina Xu)