logo

HAUSA

Hukumar CONCACAF za ta yiwa tsarin neman gurbin buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya kwaskwarima

2019-07-17 10:27:50 CRI

Hukumar CONCACAF mai lura da harkar kwallon kafar yankunan arewaci da tsakiyar Amurka da yankin karebiya, za ta rage kusan rabin wasannin da ake bugawa a matakin yankunan da take iko da su, na neman gurbin buga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya. Hukumar ta ce, daga yanzu ba za a sake buga zagayen farko na rukuni mai kasashe 6 ba. Maimakon haka daga watan Satumba mai zuwa, kasashe 6 mafiya kwarewa a taka leda a yankunan, za su buga wasannin neman gurbi tsakanin su, kana 3 da suka yi nasara za su samu damar buga gasar cin kofin duniya kai tsaye, wadda za ta gudana a Qatar a shekarar 2022. A yanzu dai kasar Mexico ce ke saman rukunin kasashen yankunan mafiya kwarewa a fagen taka leda bisa kiyasin hukumar FIFA, kuma ita ce ta 18 a duniya baki daya. Sai kuma Amurka wadda ita ce ta 30 a duniya, sai Costa Rica ta 39 a duniya. Sauran sun hada da Jamaica mai matsayi na 54 a duniya, da Honduras mai matsayi na 61 a duniya, da kuma El Salvador dake matsayi na 69 a duniya. A daya bangaren kuma, hukumar za ta gudanar da wata gasar ta daban, domin kasashen dake matsayin da bai kai na farkon ba, bayan hakan ne kuma wadanda suka yi nasara za su hadu da 6 da aka zaba a matakin na sama. Ta haka ne kuma za a kai ga ware karin kasashen da za su wakilci sassan yankin a gasar ta kasar Qatar.

A takaice dai CONCACAF ta rage yawan wasannin da sassan yankunan uku suke bugawa daga kasashe 18 zuwa 10, kafin fitar da wadanda za su kai ga buga gasar duniya da hukumar FIFA ke shiryawa.(Amina Xu, Saminu)