logo

HAUSA

Lyu Sunhao matashin dan kwallo dake fatan zama tauraro a Argentina

2019-07-11 17:27:50 CRI

Matashin dan wasan kwallon kafa daga kasar Sin Lyu Sunhao, daya ne daga matasa dake fatan ganin sun kafa tarihi a duniyar kwallon kafa. Saurayin mai shekaru 15 da haihuwa, yanzu haka ya fara samun horo a Argentina, kasar da ta fitar da manyan taurarin kwallon kafa irin su Lionel Messi. Yayin wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, matashi Lyu ya ce burin sa shi ne taka leda a Argentina, ta yanda nan gaba zai zamo dan kwallon kafa na farko daga kasar Sin, da zai buga kwallo a ajin kwararru a kasar dake kudancin Amurka, sa'an nan ya koma gida Sin domin shiga a dama da shi a babbar kungiyar kasar. Lyu ya ce Messi ne tauraron sa da ma yawanci Sinawa a kwallon kafa. Tuni dai matashin ya shafe wata guda a birnin Buenos Aires, inda yake zaune a rukunin gidajen da aka tanadarwa 'yan wasan kulaf din Atletico River Plate, daya daga manyan kulaflikan ajin matasa na Argentina. Yankin mai makwaftaka da Belgrano, 'yan mitoci daga filin wasa na Monumental, ya kasance sansani na matasan 'yan wasa dake buga kwallo a kulaflika daban daban na duniya. Lyu ya kara da cewa "Ina matukar farin ciki da kasancewa ta a Argentina. River daya ne daga manyan kulaflika a duniya, zan kuma yi amfani da wannan dama wajen samun cikakkiyar gogewa. Ya ce "yanzu dai ba abun da ke wahalar da ni kamar rashin fahimtar yare," ko da yake a cewar sa tuni ya fara gane wasu kalmomi da ake amfani da su a kwallon kafa na yaren Sifaniyanci, kamar "pase corto" (mika kwallo kadan), "pase largo" (mika kwallo mai tsawo), "cabezazo" (sa kai), "punto penal" (layin bugun daga kai sai mai tsaron gida) da kuma, burin rayuwar sa a takaice, "partido de futbol" (Kwallon kafa). "Pucca," kamar dai yadda abokan wasan sa ke kiran sa, wani suna da suka saka masa daga wani tauraron wasan Cartoon na kasar Koriya ta kudu, ga dukkanin alamu yana da jinin kwallon kafa tare da shi. An haifi Lyu a binrin Ningbo dake gabashin lardin Zhejiang, ya kuma samu matukar sha'awar sa ga kwallon kafa ne sakamakon kaunar da baban sa Mr. Gao Xin ke yiwa wasan, inda har ta kai shi ga horas da matasan 'yan wasa da dama wannan wasa. Yanzu dai Lyu wanda dan wasan tsakiya ne, ya sanya hannu kan kwantiragin shekara daya a wannan kungiya ta kwallon kafa, yana kuma kammala ka'idojin shige da fice, kafin a gabatar da shi ga kungiyar baki daya. Da yake tsokaci game da dan wasan, daya daga koci dake horas da 'yan wasa matasa Jorge Gordillo, ya ce Lyu na kara sabawa da yanayin sabon wurin da ya isa. Yana gane umarnin da ake yi masa nan da nan, duk da banbancin yare, kuma hakan alamu ne na yaro mai hazaka. Gordillo shi ma ya taba taka leda a gasannin Intercontinental Cup, da Copa Libertadores a shekarar 1986, tare da taurarin 'yan wasa irin su Nery Pumpido, da Oscar Ruggeri, da Hector Enrique, da Norberto Alonso, da Antonio Alzamendi, ya ce Lyu ya samu wata kyakkyawar dama ta koyon salon kwallon kudancin Amurka, musamman sarrafa kwallo cikin gwaninta a filin wasa. Ya ce "a nan samarin 'yan wasa na da zarafin buga kwallo a wuri mai nutsuwa, irin wanda da yawa daga yaran sassan wasu kasashe ba sa samu, kamar dai Lyu, wanda ya zo daga Sin. Kocin ya kara da cewa, daga irin wannan yanayi ne kuma ake kaiwa ga matsayin buga gasanni, da gogewar da za ta baiwa dan wasa damar yin fice a manyan gasanni. Shi kuwa a nasa tsokaci, wani jami'in dake hidimar hada 'yan wasa da kulaflika musamman wadanda aka haifa a Argentina amma iyayen su 'yan asalin nahiyar Asiya ne mai suna Mr. Luis Xu, ya ce kudurin kasar Sin na bunkasa harkar wasan kwallon kafa, zai taimaka wajen fitar da karin Sinawa zuwa manyan kulaflikan duniya. Ya ce "Abu ne mai kyau 'yan wasan su fito daga Sin zuwa kasashe irin su Argentina, duba da cewa tuni Messi ya yayata harkar kwallon Argentina a dukkanin sassan duniya, ta yadda wasan ya dada samun karbuwa a ko ina.

Lyu, wanda a bara ya yi atisaye na watanni 3 a kungiyar UAI Urquiza, ita ma ta Argentina, dake buga matsayi na 3, ya amince da wannan ra'ayi. Ya ce "A nan, bukatar kwarewa tana da yawa, ana matsawa sosai, yanayi ne da ya saba da na wasu wuraren".(Saminu Alhassan)