logo

HAUSA

Safinatu Mukhtar Kaita

2019-07-09 11:18:38 CRI

Safinatu Mukhtar Kaita

Yau shirin In ba ku ba gida na farin cikin gabatar muku wata muhimmiyar bakuwa daga tarayyar Najeriya, wato Hajiya Safinatu Mukhtar Kaita, wadda ke aiki a kwamitin bincike da raya albarkatu da sinadaran da ake sarrafawa da ke Abuja. A 'yan kwanakin baya, Hajiya Safinatu da abokan aikinta sun zo kasar Sin don halartar taron kara wa juna sani kan musayar fasahohi a tsakanin Sin da kasashen Labarawa.

A cikin zantawar da wakiliyarmu Fa'iza Mustapha ta yi da ita, Hajiya Safinatu ta yi bayani kan makasudinsu na halartar wannan taron na neman damammakin da za su amfana wa ci gaban Najeriya. Bugu da kari kuma, a matsayinta ta mace, a cikin wannan shirin namu na "In ba ku ba gida", Hajiya ta yi tsokaci kan kokarin mata wajen koyon kimiyya da fasaha, da ma gudummawar da mata ke bayarwa ga ci gaban zamantakewar al'umma ban da aure, reno da kula da gida.(Kande Gao)