logo

HAUSA

Sabon shiga Madagascar ta tashi da 2-0 da Najeriya a gasar AFCON

2019-07-04 14:27:12 CRI

Madagascar, sabon shiga a gasar cin kofin kwallon kafan Afrika (AFCON), ta bada mamaki inda ta doke shahararriyar kungiyar kwallon kafan Najeriya da ci 2-0 a ranar Lahadi. Dan wasan tsakiyar Madagascar Lalaina Nomenjanahary shine ya fara zara kwallo mintoci 13 da fara wasan yayin da Carolus Andriamatsinoro ya zura kwallo ta biyu bayan mintoci 53 da fara wasan, koda yake, Najeriya ta samu kashi 62 bisa 100 na maki a gasar kwallon kafar. Madagascar da Najeriya sun kai matsayi na 16 a rukunin B inda Guinea ta samu damar haduwa dasu a matsayin wata muhimmiyar dama a karo na uku domin samun maki 4. Burundi, kasa ta 4 dake rukunin B, ta rasa dukkan wasanninta 3. Gasar AFCON ta 2019 ta samu kungiyoyin wasa 24 a karon farko maimakon kungiyoyi 16 a bisa tarihin gasar. A zagaye na 16 za'a samu kasashe 2 dake sahun gaba a rukunoni 6, sai kuma kasashe 4 dake sahun gaba wadanda zasu shiga zagayen karshe na gasar

Gasar AFCON karo 32 an budeta ne a kasar Masar a ranar 21 ga watan Yuni za'a kammala zuwa 19 ga watan Yuli.(Amina Xu, Ahmad)