Masar ta doke Uganda da 2-0 inda ta kai matsayi na 16 a gasar AFCON
2019-07-04 14:30:54 CRI
Kasar Masar mai masaukin baki ta doke Uganda da ci 2-0 a wasan da suka buga a yammacin Lahadi na gasar cin kofin kasashen Afrika (AFCON), lamarin da ya bata damar shiga rukunin A da maki 3 a gasar. Shahararren dan wasan Masar na kungiyar wasan Liverpool, Mohamed Salah, shine ya fara budewa da zara kwallo mintoci 36 da fara gasar, sai kuma dan wasan tsakiyar kungiyar Ahmed Elmohamady ya zara kwallo ta biyu gabanin tafiya hutun rabin lokaci. Da yake bayani game da wasan, Elmohamady ya fadawa manema labarai cewa, kungiyarsa tayi wasa tukuru, ya kara da cewa, kungiyar wasan kasar Uganda ta kusan zara musu kwallo, amma kungiyar wasan ta sanyawa gidanta kyawawan matakan tsaro. "Tuni mun riga mun fara shiye shiryen shiga zagaye na 16 na gasar kuma muna sa ran kaiwa matsayin daukar lambar yabo," injishi. Masar ce ke sahun gaba a gasar ta AFCON, sakamakon samun lambobin yabo sau 7 a tarihi, wanda ya hada da sau uku a jere, na baya bayan nan shine na shekarar 2010. Uganda zata halarci zagayen wasan kifuwa daya kwale bayan da ta jagoranci rukunin A da maki hudu, yayin da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo ta zo ta uku da maki uku, sai Zimbabwe data yi bankwana da gasar bayan da ta samu maki daya kwal a gasar. Gasar AFCON ta 2019 ta samu kungiyoyin wasa 24 a karon farko a maimakon kasashe 16 dake shiga gasar. Rukunin wasan kifuwa daya kwale a rukuni na 16 wanda ya kunshi manyan kungiyoyin wasa biyu a rukunonin 6 da kuma hudun dake sahun gaba a zagaye na 3.
Wasan wanda ake gudanarwa a Masar a karo na 5, shine wasan kwallon kafa mafi shahara na nahiyar Afrika wanda aka bude a ranar 21 ga watan Yuni za'a kammala a ranar 19 ga watan Yuli(Amina Xu, Ahmad)