An fitar da kungiyoyi 16 a sabon zagaye na gasar cin kofin kasashen Afirka
2019-07-04 14:37:03 CRI
An kammala dukkan gasanni a wasan rukuni-rukuni na gasar cin kofin kasashen Afirka a jiya, an fitar da kungiyoyi 16 a sabon zagaye na gasar.
Kungiyar wasan Mali ta kai matsayi na farko a rukunin E, kana Tunisia tana matsayi na biyu a rukunin, Angola da Mauritania sun samu matsayi na uku da na hudu, amma makin da Angola ta samu ya fi karanci idan aka kwatanta ta na sauran rukuni, don haka Angola ba ta shiga sabon zagaye ba.
A rukunin F, kungiyar Ghana ta samu nasara a gasar karshe ta wasannin rukuni, ta zarce Kamaru domin karin kwallayen da ta ci ta zama matsayin farko a rukunin, kuma Kamaru ta zaman ta biyu.
Za a gudanar da sabon zagayen gasar tun daga ranar 5 zuwa 8 ga wannan wata, Morocco za ta buga wasa da Benin, Uganda za ta yi da Senegal, Nijeriya za ta fafata da Kamaru, Masar da Afirka ta Kudu za su buga wasa, kuma sauran gasannin da za a gudanar sun yi a tsakanin Madagascar da Congo Kinshasa, Algeria da Guinea, Mali da Cote d'Ivoire, Ghana da Tunisia. (Amina Xu, Zainab, Ahmad)