Sudan ta kudu ta nada Besong na jamhuriyar Kamaru a mtsayin sabon kociyanta
2019-07-04 14:28:45 CRI
Kungiyar wasan kwallon kafar Sudan ta kudu (SSFA) a ranar Litinin ta nada Ashu Cyprian Besong dan kasar Kamaru a matsayin sabon mai horas da 'yan wasan babbar kungiyar wasan kwallon kafan kasar. Besong, wanda ya taba jagorantar tawagar 'yan wasan Kamaru 'yan kasa da shekaru 20, zai maye gurbin mai rikon mukamin kociyan kungiyar na wucin gadi Ramzi Sebit, inji SSFA. "Ashu Cyprian Besong na jamhuriyar Kamaru zai kasance a matsayin sabon kociyan kungiyar wasan kwallon kafan Sudan ta kudu. An tabbatar cewa zai isa birnin Juba, a ranar Talata domin karbar sabon aikin da aka bashi," inji jami'an hukumar wasan ta SSFA wanda suka bayyana ta shafinsu na Facebook. An bar gurbin mukamin kociyan ba tare da nada kowa ba tun a watan Satumbar 2018, tun bayan murabus din da Ahcene Ait-Abdelmalek dan kasar Algeria yayi watanni 7 bayan nadashi kan mukamin. Besong ya kasance kociyan Sudan ta kudu na biyar bayan tafiyar Ait-Abdelmalek, da Lee Sung-Jea dan Koriya ta kudu, da Serbian Zoran Dordevic da kuma Uganda's Leo Adraa.
Kasar mafi yarinta a duniya ta gaza samun nasara a wasannin share fagen shiga gasar cin kofin Afrika ta 2019 (AFCON) a Masar, inda ta rasa dukkan wasanninta na share fagen data buga a rukunin C. (Amina Xu, Ahmad)