Ranar kasa da kasa ta yaran Afirka
2019-06-27 08:34:22 CRI
Ranar 16 ga watan Yunin ko wace shekara, rana ce da ake gudanar da bikin ranar kasa da kasa ta yaran Afirka, wadda ke ba da damar yayata manufar inganta samar da ilimi ga yara dake sassan nahiyar daban daban. An dai fara kudanar da bikin ranar yaran Afirka ne tun daga shekarar 1991, inda a wancan lokaci kungiyar hadin kan nahiyar Afirka ta OAU, wadda ta sauya suna zuwa AU a yanzu ta kaddamar da ita.
OAU ta ware wannan rane ne domin tunawa, da martaba dubban matasa bakaken fata da suka gudanar da zanga zanga a shekarar 1976 a Soweton Afirka ta kudu, suna masu bukatar inganta yanayin ilimi, da ba su damar koyon karatu da harshen gida. Wannan zanga zanga dai ta kai ga jami'an tsaron kasar sun hallaka sama da mutum 100 cikin masu zanga zangar, lokacin da jami'an tsaron suka bude musu wuta.
Ko shakka ba bu, batun muhimmancin ilimi ya wuce koyon karatu da rubutu kawai, domin kuwa ya hade sassan rawar da ilimin ke takawa, wajen wayar da kan al'umma, ta yadda za su kauracewa munanan hanyoyi na rayuwa, kama daga rashin baiwa yara kulawar da ta dace, da kaucewa bautar da yara, da kaucewa cin zarafin su ko dai ta hanyar lalata, ko shigar da su kungiyoyin ta'addanci da na 'yan tada kayar baya, da hana musu damar samun ilimi mai nagarta, kai har ma da samar da ingantaccen tsarin raya sana'oi, da tsarin kiwon lafiya mai dorewa. Wasu alkaluma da hukumomi masu ruwa da tsaki suka fitar a baya bayan nan, sun nuna cewa, akwai yara da shekarun su suka kai na shiga makaranta, amma ba su samu damar shiga makarantu ba, saboda dalilai na yake yake, da rikice rikice da ke raba su da muhallan su, ko ma wadanda ke mayar da yaran marayu. Wasu alkaluma sun nuna cewa, yawan irin wannan rukuni na yara a fadin duniya ya kai miliyan 57, kuma sama da rabin su na rayuwa ne a yankunan kudu da hamadar Saharar Afirka.
Wadannan da ma sauran dalilai dake almata irin halin ni-'ya-su da yara ke fuskanta a nahiyar ne, suka sanya gwamnatocin kasashen nahiyar, da kungiyoyi masu zaman kan su, da na kasa da kasa, da sauran masu ruwa da tsaki, ke amfani da ranar 16 ga watan na Yuni, wajen fadakar da juna irin kalubale, da damammaki, da kuma burin yaran Afirka na samun kariyar 'yancin su, da damar su ta samun ilimi mai nagarta.
Yanzu haka ranar yaran Afirka ta wuce batun ranar biki kadai, rana ce dake samar da damar fadakar da al'ummar nahiyar, irin bukatar da ake da ita, ta ci gaba da bunkasa hanyoyin samar da nagartaccen ilimi ga manyan gobe, bukatar da kawo yanzu muhimmancin ta ba ya misaltuwa. (Saminu, Ahmad, Sanusi)