logo

HAUSA

Yatulla Zara Baba Ahmad Jidda, matar jakadan Najeriya a Sin

2019-06-25 16:23:34 CRI

 

Yatulla Zara Baba Ahmad Jidda, matar jakadan Najeriya a Sin

Yau shirin In ba ku ba gida na farin cikin gabatar muku wata muhimmiyar bakuwa daga tarayyar Najeriya, wato Hajiya Yatulla Zara Baba Ahmad Jidda, shugabar kungiyar matan kasashen renon Ingila ta Beijing, kuma matar Jakadan Tarayyar Najeriya dake kasar Sin. A makon da ya gabata ne, kungiyar kasashen renon Ingila ta Beijing ta shirya wani bikin bada sadaka, wakiliyarmu Fa'iza Mustapha ta halarci bikin, inda kuma ta samu damar yin hira tare da Hajiya Yatulla.

A cikin hirarsu, Hajiya Yatulla ta yi bayani kan wannan kungiyar, da kuma kokarin da take yi don kyautata aikin kungiyar a matsayinta na shugaba. Kana ta musunta zargin da ake cewa kasar Sin na danawa Najeriya tarkon bashi. Bugu da kari kuma, a matsayinta ta mace, a cikin wannan shirin namu na "In ba ku ba gida", Hajiya ta kwatanta matan Sin da na Najeriya, da kalubalen da matan Najeriya ke fuskanta wajen fita daga gida.  (Kande Gao)