An zabi Infantino a matsayin shugaban FIFA a wa'adi na 2 na shekaru 4
2019-06-13 15:10:30 CRI
Shugaban hukumar kwallon kafann duniya FIFA Gianni Infantino ya gabatar da jawabi a lokacin babban taron hukumar FIFA karo na 69 a birnin Paris, na kasar Faransa a ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2019. Sama da shekaru 3 tun bayan da ya karbi shugabancin hukumar domin maye gurbi tsohon shugaban hukumar ta FIFA Sepp Blatter, wanda aka zarga ta laifin ayyukan rashawa, Gianni Infantino, ya samu tabbacin lashe zaben na FIFA da kuri'un mambobi 211, an sake zabarsa a ranar Laraba a matsayin shugaban hukumar kwallon kafan duniya inda zai jagoranci hukumar. Jami'in dan shekaru 49 dan kasashen Swiss-Italian, shine babban dan takara dake neman wa'adin shugabancin hukumar na 2019-2023, kuma an gudanar da babban taron na FIFA ne bisa al'ada don cike gurbi a karo na 69. Yayi alkawarin ba zai zura ido yana kallo tamkar gunki ba sai dai zai mayar da hankali ne wajen bunkasawa da kuma kare martar harkokin wasan kwallon kafa, Infantino ya furta hakan ne a karshen jawabinsa yace babban abinda zai fi mayar da hankali shine samar da yanayin gogayya a tsakanin matasa, domin cigaba da bunkasa cigaban kwallon kafa ta mata da kuma shirya wasu dokoki da zasu shafi cigaban kwallon kafa a duniya. Gabanin sanar da zabensa, Infantino ya yi jawabi a dunkule kan irin nasarorin da FIFA ta cimma karkashin jagorancinsa, bayan da aka dora masa alhakin farfado da kimar hukumar wasan kwallon kafan tun bayan sauke mutumin da ya gada wato Blatter wanda ake tuhuma da zarge zarge masu yawa da suka shafi ayyukan rashawa. "A yau babu wani mutum dake magana game da matsaloli, babu wanda ke magana akan sake gina hukumar, babu wanda yake magana game da rashawa. "Mun riga sun sauya dukkan al'amurra. FIFA ta yi nisa daga halin magagi data shiga, da matsayin bata gari, zuwa matsayin hukumar bunkasa harkokin kwallon kafa," injishi.
Ya karbi ragamar shugabancin ne daga hannu Blatter da ya tafka abin kunya a watan Fabrairun shekarar 2016, Infantino ya gabatar da shirin VAR a 2018 lokacin gasar cin kofin duniya a Rasha kuma ya kara kaimi wajen inganta wasan kwallon kafan mata zalla a daidai lokacin da yake tsaka da yaki da ayyukan rashawa.(Amina Xu,Ahmad)