logo

HAUSA

An samu babban ci gaba yayin da ake raya babban yankin Jing-Jin-Ji na kasar Sin

2019-06-10 08:39:26 CRI

An samu babban ci gaba yayin da ake raya babban yankin Jing-Jin-Ji na kasar Sin

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanmu da sake kasancewa a cikin sabon shirinmu na "Allah daya gari bamban", shirin dake zuwa muku kai tsaye daga nan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin tare da ni Jamila, to a yau za mu yi muku bayani kan babban ci gaban da aka samu yayin da ake kokarin raya babban yankin Jing-Jin-Ji wanda ya kunshi birnin Beijing da birnin Tianjin da kuma lardin Hebei.

Bana wato shekarar 2019, shekaru biyar ke nan da aka fara aiwatar da manufar raya babban yankin Jing-Jin-ji cikin hadin gwiwa, a cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata, ana gudanar da manyan ayyuka da dama lami lafiya, haka kuma an samu babban ci gaba a bayyane yayin da ake kokarin raya babban yankin, ana iya cewa, za a a cimma burin da aka tsara wato raya babban yankin cikin hadin gwiwa kamar yadda ake fata.(Jamila)