logo

HAUSA

Taron inganta muhalli na MDD

2019-06-06 09:18:21 CRI

MDD ta bude taro na farko game da muhallin halittu, domin warware kalubalen da ake fuskanta yayin da ake raya birane a sassan duniya daban daban.

Taron wanda aka bude a ranar Litinin 28 ga watan Mayun shekarar 2019, a birnin Nairobin kasar Kenya, ya hallara mahalarta sama da 3,000, ciki hadda shugabannin kasashe hudu, da sama da ministocin kasashe 40, da manyan wakilan wasu karin kasashen duniya 116, inda aka tattauna game da dabarun inganta rayuwar al'umma mazauna birane, a dai-dai lokacin da biranen duniya ke dada dunkulewa waje guda.

Taken taron na wannan karo shi ne "kirkire kirkire domin inganta rayuwa a birane da ta al'ummu".

Da take jawabi yayin bikin bude taron, babbar daraktan hukumar UN-Habitat mai lura da muhallin halittu Maimunah Mohd Sharif, ta ce akwai hasashen dake nuna cewa, nan da shekarar 2050, kaso 70 bisa dari na al'ummun duniya za su rika rayuwa ne a birane, wanda hakan ka iya haifar da wasu sabbin kalubale ga wasu kasashen a fannin samar da muhimman ababen more rayuwa, kamar gidajen kwana, da sufuri, da ayyukan yi, da ilimi, da lafiya da dai sauran su.

A don haka masu fashin baki ke kira ga mahukunta, da su sanya batun gina ingantattun birane masu dorewa, a matsayin jigon kudurorin ci gaban kasashen su. Kaza lika su aiwatar da sabbin dabarun kyautata birane, da karfafa tsarin gudanar da birane, da tsarin wanzar da ci gaban birane bayan kafuwar su. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)