logo

HAUSA

Masar ta fitar da mutum mutumin dake alamta gasar cin kofin Afirka na 2019

2019-05-30 14:58:07 CRI

Hukumar kwallon kafar kasar Masar, ta fitar da mutum mutumin dake alamta gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka ta AFCON ta bana wanda za ta karbi bakuncin sa. A ranar Lahadi ne hukumar ta fitar da sanarwa mai dauke da hakan. mutum mutumin dai an sanya masa suna TUT, kuma ya yi kama da sarkin kasar na zamanin da, wanda aka kawata da kayan ado. Sanarwar ta ce "Bayan tsawon lokaci, ga shi muna gabatar muku. Ku yi maraba da babban mai saukar bakin gasar AFCON ta 2019". A watan Janairu, hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta bayyana sunan kasar Masar a matsayin wadda za ta karni bakuncin babbar gasar nahiyar a karo na biyar a tarihin ta. An kuma tsara gudanar da gasar ne tsakanin ranekun 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli, bayan da aka karbe ikon karbar bakuncin gasar daga kasar Kamaru. An ce Kamarun ta gaza ne wajen tabbatar da shirye shiryen da ake bukata na gudanar gasar. Kafin Masar ta samu wannan dama, ta yi takara da Afirka ta kudu, inda daga karshe ta samu damar karbar bakuncin gasar da kuri'u 16, yayin da Afirka ta kudu ta samu kuri'u 2. Masar ta karbi bakuncin wannan gasa ta nahiyar Afirka a shekarun 1957, da 1974, da 1986 da kuma 2006, ta kuma lashe gasar har karo 7. A bana an bullo da sabbin abubuwa game da gasar, ciki hadda fadada yawan kungiyoyin da za su shiga a dama da su daga kasashe 16 zuwa 24, aka kuma matsar da gasar zuwa lokacin bazara, sabanin tsakanin wanannin Janairu zuwa Fabarairu da ake gudanar da ita a baya, domin kaucewa karo da bukatun 'yan wasan nahiyar ta Afirka dake buga gasannin kulaflikan nahiyoyin turai. Tuni dai hukumar kwallon kafar kasar ta Masar ko EFA a takaice, ta sanar da ware filayen wasa guda 6 domin gudanar da gasar dake tafe, ta kuma rufe su domin fara gyare gyaren da suka wajaba. An tsara bude gasar AFCON ta bana, a filin wasa na birnin Alkahira mai cin 'yan kallo 74,100, inda mai masaukin baki Masar za ta kece raini da takwarar ta ta kasar Zimbabwe. Da yake karin haske game da hakan, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, jami'i a hukumar ta EFA Magdi Abdel Ghani, ya ce samun wannan dama babban al'amari ne ga kasar Masar. Kuma hakan na aika wani sako mai karfi dake nuna cewa, akwai zaman lafiya da lumana a Masar, kuma kasar na da cikakken ikon karbar bakuncin wannan gasa.

Magdi Abdel Ghani wanda ya taba taka leda a kungiyar kasar ta Masar, ya ce kasar sa na da dukkanin abubuwan da ake bukata domin karbar bakuncin gasar, tana da kuma kwarewa wajen shirya gasar, wadda take mafi girma a nahiyar Afirka, gasar da za ta tara al'ummar da yawan su ya kai miliyan guda.(Amina Xu, Saminu)