logo

HAUSA

Africa za ta fidda kasashen da za su wakilce ta a gasar kwallon zari ruga ta duniya ajin mata karo na 15

2019-05-30 14:49:57 CRI

Yanzu haka shirye shirye sun yi nisa, na gudanar da wasannin fidda kungiyoyin kasashen Afirka, da za su wakilci nahiyar a gasar kwallon zari ruga ko Rugby ajin mata ta duniya, wadda za a buga a kasar New Zealand a shekarar 2021. Za dai a buga wasannin samun gurbin gasar ta duniya ne a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, tsakanin ranekun 9 zuwa 17 ga watan Agustan wannan shekara, kuma kungiyoyin kasashen Afirka ta kudu, da Kenya, da Uganda da Madagascar ne za su buga wasannin. Gasar fidda kungiyoyin kasashen da za su wakilci nahiyar Afirkan ta bana, za ta zamo dama da za ta baiwa kungiyar da ta yi nasarar lashe gasar, ikon daga kofin nahiyar, kana ta samu gurbin buga gasar duniya ta 2021. Duk da yake ba wani tsari na musamman na fidda jerin kasashe mafiya kwarewa na gasar Rugby a nahiyar Afirka, amma mashirya gasar sun zabi kungiyoyin nahiyar guda 4 ajin mata, saboda yawan halartar wasan da suke yi a baya. Da yake karin haske game da hakan, babban manajan hukumar shirya wasannin kwallon ta zari ruga ko Rugby ajin mata ta kasa da kasa Katie Sadleir, ya ce wannan wata dama ce ga nahiyar Afirka, wadda bai kamata ta a yi wasa da ita ba. Sadleir ya ce bunkasar wasan rugby babbar dama ce ga harkar wasanni a cikin shekaru goma masu zuwa. Ya ce shigar Afirka gadan gadan cikin wannan wasa, ya nuna yadda wasan ke zama na kowa da kowa, da ma burin wasan na karade dukkanin sassan duniyar nan. Jami'in ya ce, kwallon Rugby ajin mata na samun manyan sauye sauye, da ci gaba mai armashi a dukkanin matakai. Kaza lika kwallon ta rugby a Afirka, na jagorantar wannan ci gaba da ake samu, duba da yawan mata 'yan wasan dake taka leda a kungiyoyin kasashen duniya daban daban. Kungiyoyin kasashen 4 da za su buga wasa a matakin nahiyar Afirka, za su fitar da zakaran da zai wakilci nahiyar a gasar kasa da kasa ta Zealand a shekarar 2021. A matakin nahiyar, dukkanin kasashen da suka samu shiga gasar su 4, za su buga wasanni uku uku, kana a fitar da kungiyar da ta yi nasara da yawan maki, wadda kuma za ta samu gurbin shiga gasar ta duniya kai tsaye. An kuma ce kasar da ta zo ta biyu, za ta buga karin wasa da wata kasa daga nahiyar kudancin Amurka, idan ta samu nasara kuma, sai ta shiga jerin kasashen da za su buga gasar ta duniya. A nasa tsokaci, shugaban hukumar kwallon Rugby ta nahiyar Afirka Khaled Babbou, ya ce nasarar kwallon a nahiyar Afirka, na cikin manyan manufofin da suke son cimmawa. Ya ce shirya wasannin samar da gurbin shiga gasar cin kofin kwallon zari ruga ta kasa da kasa, ya samar da wani zarafi na baiwa 'yan wasan dake buga kwallon dama, ta kaiwa ga matsayi mafi girma a wasan. Jami'in ya kara da cewa, ci gaban wasan Rugby shi ne burin su, kuma bunkasa rukunin gasar ajin mata, na cikin muhimman matakan cimma burin hakan. Khaled Babbou, ya kara da cewa, wasan rugby ajin mata har yanzu yana kara bunkasa a nahiyar Afirka, kuma hanya daya tilo ta daga matsayin wasan ita ce samar da damar fuskantar kungiyoyin kasa da kasa a gasa. A watan Mayun nan ne dai hukumar kwallon Rugby ta kasa da kasa, ta shirya wani taron masu ruwa da tsaki a birnin Gaborone na kasar Botswana, inda a lokacin ne aka tsara yadda za a gudanar da gasar ajin mata ta nahiyar Afirka bisa yankuna, da tattalin arzikin kasashe, da kuma al'adun nahiyar ta Afirka.

Babban burin shirya gasar dai a cewar mashiryanta shi ne, yayata wasan tsakanin mata. A mataki na kasa da kasa kuwa, kungiyoyi 12 ne za su kece raini a gasar da New Zealand za ta karbi bakunci, inda a karon farko aka kai gasar yankin kudancin turai.(Amina Xu,Saminu)