Yadda takaddamar cinikayyar Sin da Amurka ta sake daukar salo
2019-05-23 19:11:15 CRI
Yanzu haka dai, takaddamar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ta dauki wani sabon salo, baya ga matakin kara haraji na kaso 25 cikin 100 kan kayayyakin da kasar Sin take shigarwa cikin kasar Amurka da darajarsu ta kai dala biliyan 300 da ya fara aiki. Wai bisa dalili Sin ta mayar da martani kuma ba ta gyara wasu matakanta a fannin ciniki ba.
Sai dai duk da matakin da Amurka ta dauka na tayar da yakin ciniki mafi girma a tarihin duniya, kasar Sin ta gabatar da matakai daban-daban domin sassauta matsalolin da yakin cinikin zai haifar wa kamfanoni da al'umma. Wadanda suka hada da, nazarin tasirin da yakin zai haifar wa kamfanoni. Sa'an nan kuma, a yi amfani da karin harajin da aka tara wajen sassauta kalubalolin da yakin ya haifar wa kamfanoni da ma'aikatansu. Daga bisani kuma, a sa kaimi ga kamfanonin da su daidaita tsarinsu na shigar da hajoji daga ketare.
A karshe, a gaggauta aiwatar da manufofin da gwamnatin kasar Sin ta fitar na yin amfani da jarin da kamfanonin ketare suka zuba yadda ya kamata, inganta bunkasuwar tattalin arziki mai inganci, kara aikin kare 'yancin kamfanoni bisa doka da kuma kyautata yanayin zuba jari a kasar Sin da sauransu.
Mataki na baya-bayan da Amurka ta dauka dangane da takaddamar cinikayyar sassan biyu, shi ne wanda ya karkata ga kamfanin sadarwa na Huawei,duk da jerin tattaunawa kusan 11 da jami'an sassan biyu suka gudanar a lokuta daban-daban da ma shawarwari da sharhuna da masana ke bayarwa kan yadda za a magance wannan matsala, inda kamfanin Google ya hana kamfanin Huawei amfani da manhajar Android, sai dai kamfanin ya ce, yana da karfin tunkarar wannan matsala.
Kamar yadda wasu masana suka ce, kara harajin kwastan kan hajojin kasar Sin da kasar Amurka ta yi, zai haddasa babbar matsala ga kamfanonin kasar Sin da abin ya shafa, har ma ga rayuwar ma'aikatan wadannan kamfanonin. Gwamnatin kasar Sin ta san da hakan, shi ya sa, ba ta son tayar da yakin ciniki tun farko. Amma, ya kamata kasar Sin ta mayar da martani ga yakin cinikayyar Amurka.
Masu fashin baki na cewa, gwamnati Amurka tana kokarin saka duniya cikin matsalar da babu wanda ya san irin mummunan sakamakon da za ta haifar a nan gaba. ( Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)