Hira da Farfesa Salisu Ahmed Yakasai daga Najeriya
2019-05-17 14:29:25 CRI
A wannan mako, za ku ji wata hira da muka yi da Farfesa Salisu Ahmed Yakasai, wato malami a jami'ar Usman dan Fodio dake Sokoto a tarayyar Najeriya, wanda a halin yanzu yake gudanar da aikin koyarwa a jami'ar koyon harsunan kasashen waje ta Beijing dake nan kasar Sin, ya yi tsokaci game da yadda harshen Hausa ke samun bunkasuwa a fadin duniya, da kuma yadda harshen Hausa yake kara kyautata dangantaka tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya ta fannoni da dama. Ga cikakkiyar hirar.